Labaran Kannywood

Duk wanda yasha rubutu yasha datti kuma zai iya kamuwa da cutar Typhoid – Sheikh kabiru gombe

Sheikh Kabiru Gombe: Duk wanda yasha Rubutu ya sha datti kuma zai iya kamuwa da Typhoid,malam yayi bayyani

Fitaccen malamin addinin Muslunci Sheikh kabiru Muhammad gombe yayi wani bayyani akan shan rubutu da mutane suke cewa.

Shafin sawtul hikima sun wallafa bidiyon shafinsu na tiktok inda malam yake bayyani.

Sheikh Kabiru Gombe:Duk wanda yasha Rubutu ya sha datti kuma zai kamuwa da Typhoid,malam yayi bayyani
Sheikh Kabiru Gombe:Duk wanda yasha Rubutu ya sha datti kuma zai kamuwa da Typhoid,malam yayi bayyani
Ga abinda malam yake cewa:

“Sai kaga wani wai ba haka kawai muke zaunawa lafiya ba kullum sai an rubuta min “wallahu galibum ala amrihi ” sai an rubutamin kafa dubu daya da dari daya da goma sha daya na shanye kasha datti, ba rubutu ka sha ba, baka dattawa da jire ka sha typhoid ka sha.

Wa ya ce maka rubutu in an wanke shi ko an goge shi sunansa rubutu , yanzu idan naje a jikin allo nayi rubutu anka share dattin wannan alli ya zubo a kasa sai ka tattara kace ae ayatul kur’siyu ce, ka zuba ruwa a kwano kasha dan kai ne mahaukaci.

To miye bambancin na dauki alli na rubuta ayyatul kur’siyu na goge da na dauki dawata da zige in rubuta ayyatul kur’siyu a allo na dauko ruwa in wanke miye banbancin su. Ai rubutu sanda yake rubuce yake rubutu , da anwake sa ya tashi daga rubutu da an goge ya tashi daga rubutun.

In kana so kasha rubutu ka hadiye allon lokacin ne kasha rubutu in kana son shan rubutu idan an rubuta maka wallahu galibum ala amrihi” sai an rubutamin kafa dubu daya da dari daya da goma sha daya to hadiye harda allon a lokacin ka sha rubutu
.”-inji sheikh kabiru Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN