Labaran duniya

Fassarar Tattaunawar Tinubu Da BBC Africa

Fassarar Tattaunawar Tinubu Da BBC Africa

Fassarar Tattaunawar Tinubu Da BBC Africa

Wakilin BBC, Peter Okochie ya Tambayi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu….

Tambaya: Mai girma yaya sha’anin kamfe ke gudana?

Amsa: Lafiya kalau. Ina da kwarin gwiwar cewa idan dai za a yi adalci a wannan zaben to zan zama a gaba.

Tambaya: Bari mu yi magana a kan abubuwan da za ka fi bai wa muhimmanci, idan ka samu sa aka rantsar da kai a ranar 29 ga watan Mayun 2023?

Amsa: Tsaro da tattalin arziki za a farfado da su da gaggawa, ta hanyar samar da aikin-yi da yi wa manufofin kudi garambawul sannan a yanke shawara dangane da batun tallafi

Tambaya: Tsaro shi ne babban
matasala. Ba zan manta a wannan dakin a 2015 an tambayi shugaba Buhari kan tsaro inda kuma ya shaida cewa ya san matsalar kuma ya san yadda zai bullo mata. Wane abu za ka yi na daban?

Amsa: Zancen gaskiya matsalar ta ragu, zan kare dangane da wannan. A baya akwai kananan hukumomi 17 a kusan jihohi 4 a Najeriya da tutar Boko Haram ke kadawa amma yanzu ba haka ba ne.
Ita fitina tashinta bai da wuya, amma kwantar da ita ba abu ne mai sauki ba. Yanzu za mu ce Buhari ya tarwatsa ISWAP duk da ba gaba daya ya gama da su ba.
Ba mu cika mayar da hankali ba a kan makaman da za su taimaka wajen dakile matsalar tsaro.
Har yanzu Yammacin turai ba su gamsu da gwamnatin Buhari ba balle su sayar mana da makamai da fasahar da muke bukata.

Tambaya: Kana tunanin hakan zai sauya al’amarin?

Amsa: E Zai iya sauya al’amari bai kuma zama lallai ya sauya ba. Amma dai dole ne mu nemo wata hanyar kamar daukar sojojin sa-kai masu yawa domin dakile matsalar.

Tambaya: ‘Yan Najeriya za su iya cewa sun fuskanci kunci a shekaru kimanin 8 da shugaba Buhari ya yi yana jagoranci, sannan kai ma yanzu jam’iyyarku daya. Shin wane abu za ka yi daban da wanda shugaba Buhari yake yi?

Amsa: Saboda ni daban nake da Buhari. sunana Bola Ahmed Tinubu. na shugabanci jihar Legas.na gina jihar da za a yi koyi da ita. ni ne na jagoranci gwamnatin da ake yin komai a fai-fai, ni ne na sauya kudin shigar da jihar take samu a cikin gida daga naira miliyan 600 zuwa biliyan biyar, wannan abun tunkaho ne, na yi maganin hankoro da kwararar teku wadda ka iya shafe mutane masu yawa a Legas, haka kuma kayan more rayuwar da na samar a Legas sun kai sun doke. Buhari ya yi iya abin da zai iya. Babu yadda zan yi in ce ba abokina ba ne kuma jagorana a jam’iyyance.

Tambaya: Idan kana magana akan kudin shiga, na san cewa kai mai kudin gaske ne ko?

Amsa: Yaya aka yi ka san hakan bayan kai ba akawuna ba ne?

Tambaya: Kana zaune a wani gidan kasaita a Legas, shin kamar ‘yan Najeriya ba su da damar sanin daga ina arzikin shugabansu yake ba?

Amsa: Shin su ‘yan Najeriya suna adawa da arziki ne? Idan ba haka ba ai sanya jari na haifar da dukiya, muna da misalin Warren Buffet mai kudin Amurka da ma duniya. Arzikina ya fara ne daga sayan hannun jari. Na gaji kasuwancin rukunin gidaje na kuma alkilta shi. Ba na gudun ace ni mai arziki ne.
Ni ne mutumin da ya fi kowa fuskantar bincike. Ni ne gwamnan jam’iyyar adawa da ya fi kowa fuskantar bincike har shekaru 8 tun daga lokacin da na hau gwamna har zuwa 2007,kuma tunda na bar ofis, ban sake karbar wani mukamin gwamnati ba. Ko kwangila.

Tambaya: To sai ana cewa a lokacin da kana gwamna kana karbar kasonka daga kudaden shiga na jihar?

Amsa: Tsahirta min! Kasona kuma? Wane kason kuma? Akwai wanda ya yi bincike ne a kaina? IMF ta yi bincike a Legas.
Mece ce matsalar jama’a ne? Kyashi ne kawai. Na ce Kyashi ne.

Tambaya: Idan da ace ba ka takarar shugaban kasa, wanne daga cikin manyan abokan hamayyarka za ka zaba tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi?

Amsa: Babu ko daya ciki!

Tambaya: Me ya sa?

Amsa: Saboda ba su dace ba. Ba su tsinana komai ba. Ni na fi su cancanta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN