Labaran duniya

DA ƊUMI ƊUMI: Za’a Rubuta Sunan Ganduje A Cikin Kundin Sunayen Mutanen Da Suka Ba Wa Musulunci Gagarumar Gudunmawa A Ƙasar Saudiyya

DA ƊUMI ƊUMI: Za’a Rubuta Sunan Ganduje A Cikin Kundin Sunayen Mutanen Da Suka Ba Wa Musulunci Gagarumar Gudunmawa A Ƙarni Na 21 A Ƙasar Saudiyya

Ƙasar Saudiyya ta duƙufa wajen tsara biki na musamman domin karrama mai girma gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a dalilin namijin ƙoƙarinsa wajen musuluntar da maguzawa sama da mutum dubu goma batare da zubar da jini ba.

A cewar mahukuntar ƙasar, abin da gwamna Gandujen ya yi wata babbar gudunmawa ce ga addinin musulunci wacce babu wani ɗan siyasa da ya taɓa ba da irinta a Afrika ta yamma gaba ɗaya a wannan ƙarni na 21 tayadda hakan ke nuni da yadda gwamnan ya cancanci yabo.

Ƙasar ta Saudiyya ta kuma ƙara da cewa a dalilin wannan ƙoƙari da gwamna Ganduje ya yi, za ta rubuta sunansa a cikin kundin tarihinta wanda ta samar domin rubuta sunayen mutanen da ke ba wa musulunci gudunmawa mai girma a Nahiyar Afrika.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ƙasar ta Saudiyya ta ke yabawa gwamna Ganduje a kan ƙoƙarinsa na hidimtawa addinin musulunci ba, ko da a baya ta taɓa karrama shi da lambar yabo mai ɗauke da ƙyallen ɗakin Ka’aba.

Sai dai a wannan karon a na tunanin salon karramawar zai sha bamban da duk wanda aka taɓa yi masa a baya girma domin kuwa gagarumin biki ne na musamman wanda ake za ra halartar manyan shugabanni na duniya.

Wane fata zaku yi masa?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN