Gwamati Taci Anarmu Yanzu Yanzu Cikin Fushi Bello Turji Yafito Yayi Zazzafan Martani Bayan Harin da Aka Kai Gidansa
Kasurgumin Dan Bindiga, Bello Turji, Ya Maida Martani Kan Harin Jirgin Sojin Najeriya
Sanannen ɗan bindigan nan, Bello Turji, ya nuna damuwarsa bisa harin da jirgin sojoji ya kai gidansa a Zamfara
Turji yace harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutanensa da dama duk da ya tuba ya rungumi zaman lafiya tsawon watanni
Ɗan bindigan ya yi gargaɗin cewa a shirye yake ya bi duk abinda gwamnati ta zaɓa tsakanin zaman lafiya da yaƙi
Zamfara – Ƙasurgumin ɗan bindigan nan, Bello Turji, yace cin amana ne harin da Sojojin Najeriya suka kai sansaninsa a jihar Zamfara.
Jaridar The Cable ta ruwaito yadda wani luguden wutan rundunar sojin saman Najeriya ya yi sanadin kashe gomman yan ta’adda a mafakar Turji.
Bayanai sun nuna cewa ‘yan fashin dajin sun halarci wurin ɗaura aure tare da Bello Turji lokacin da jirgin NAF ya yi ruwan bama-bamai a wani yankin ƙaramar hukumar Shinkafi.
Sai dai an ce Turji ya tsallake rijiya da baya. A wani faifan Audio da jaridar PRNigeria ta samu, ƙasurgumin ɗan bindigan ya nuna ɓacin ransa kan harin jirgin duk da ya amince ya watsar da ayyukan ta’addanci.
© Mai Dara Katsina Media