Gwamnatin Tinubu ta Bada Damar Shigowar Shinkafa da Sauran kayayyaki 40 da Gwamnatin Buhari ta haramta a baya
LABARI MAI DADIN JI !!!
Gwamnatin Tinubu ta Bada Damar Shigo da Shinkafa da Sauran kayayyaki 40 da Gwamnatin Buhari ta haramta a baya.
Labari mai daɗin ji ga talakawan Nijeriya: CBN ya ɗage haramcin bayar da dala ga masu safarar shigo da shinkafa Najeriya
Babban Bankin Najeriya CBN ya ɗage haramcin bayar da chanjin dala don shigar da shinkafa da wasu kayyaki 42 cikin ƙasar a wani yunƙuri na tallafa wa kasuwar musayar kuɗi na ‘lokaci zuwa lokaci’.
A shekarar 2015 ne CBN ya taƙaita bayar da dala domin shigar da wasu abubuwa ƙasar, yana mai cewa bai su kamata a bayar da dala domin shigar da su ba, kasancewar ana iya samar da su a cikin ƙasar.
To sai dai cikin wata sanarwar da CBN din ya fitar ranar Alhamis, mai ɗauke da sa hannun babban daraktan sadarwa na CBN ɗin, Isa AbdulMumin, ya ce kayyakin da ɗage wa haramcin ya shafa sun haɗar da shinkafa da sumunti da man ja da nama da kaji da sabulu da kayan kwalliya da sauran abubuwa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa a yanzu masu shigo da abubuwa 43 za su iya samun chanjin dala daga babban bankin na CBN.