Har Alkawarin kyautar inji na buga kudi aka min don na bar APC – Rarara
Shahararren mawakin nan Dauda Kahutu Rarara yayi hira da DCL Hausa tare da mai gabatarwa zaharadeen inda suke irin wannan hirar duk bayan kwanaki.
A wannan karo kuma dauda kahutu Rarara yace har tayin kyautar injimin buga kudi anyi masa idan yayiwa PDP da wata jamiya da ba sai ya fadi sunanta ba.
Rarara ya bayyana cewa anyi wannan abun ne a lokacin da Goodluck yake mulki domin kuwa a lokacin daga shi sai baban chinedu ne suka cika zaƙewa.
Idan bazaku manta rarara da Sarkin waka suna yawa fira da su inda a kwanan baya sarkin waka yace anyi masa tayin naira miliyan 150 domin bayar PDP yaki. To yau shi kuma rarara yace har tayin kyauta injin an masa ya buga kudi iya kudin da yake so amma yaki.
Hausawa kance waka a bakin mai ita yafi dadi ga bidiyon nan ku saurara.