Kannywood

Iftila’in da ya faru da tsohuwar jaruma Maryam wazeery ” Lailah Labarina” da mujinta

Tsohuwar jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Musa Waziriwadda ke amsa sunan Laila Masu Gonar Naira a tsohon shirin Labarina Series da ya gabata, tagamu da mummunar hatsarin mota a hanyar Kaduna zuwa Zariya tare da mijinta, Tijani Babangida wadda tsohon dan wasan kwallonkafar Najeriya ne, da d’an ta Muhammad Fadeelda kuma kanin mijinta, Ibrahim Babangida aranar Alhamis.

GADAI BIDIYON 👇 

Kanin mijinta, Ibrahim Babangida, shi ya ke tukamotar da su ke ciki lokacin da hatsarin ya faru,wadda kuma a take Allah Ya karbi rayuwar sa, inda aka garzaya da ita kuma Maryam da d’anta damijinta zuwa Asibiti don kula da lafiyar su.

Majiyarnmu ta Nagudu TV ta ruwaito cewa, sai dai kwana daya da hatsarin (wato a daren jiya kenan)Allah Ya yi wa karamin d’an na ta, Fadeel rasuwa shima sakamakon buguwar da ya yi.

A yanzu haka dai a cikin mutum 4 da su ka yi hatsarin, Maryam da mijinta ne su ka saura, in dasu ke karbar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika a Zariya.

Daga cikin abun da wannan hatsari ya jawo wa tsohuwar tauraruwa Maryam Waziri shine rasabangare daya na fuskar ta:

Ta rasa ido daya

Ta rasa kunne daya

Bangaren hancin ta ya gutsireGefen bakin ta ma ya gutsire

Da fatan Allah Ya jikan Ibrahim da Fadeel, Yagafarta musu. Ya bawa Maryam da TijaniBabangida lafiya. Amin.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN