Labarai

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi, rasuwa a daren jiya bayan fama da rashin lafiya

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi, rasuwa a daren jiya bayan fama da rashin lafiya. An san marigayin da iliminsa mai zurfi da kuma kokarinsa wajen yada ilimin addinin Musulunci a nahiyar Afirka.

Bayan ilimin addini, marigayin ya kasance dan kasuwa kuma manomi. A baya-bayan nan, ya yi tafiya zuwa kasashen ketare don neman magani.

Za a gudanar da jana’izarsa da misalin karfe 10:00 na safe a yau Jumu’a a Masallacin Idi na Games Village, Jihar Bauchi.

Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma ba iyalansa da al’ummar Musulmi hakurin jure wannan rashi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
KALLI BIDIYON ANAN