Labaran duniya

Innalillahee! Kalli yadda yan Boko-Haram suka kaiwa Masallata Hari yayin da suke sallah

Boko Haram sun bude wuta kan masallaci sun kashe Limami da wasu 3 a Garin Ngulde Askira Uba ta Jihar Borno

Wasu ‘yan ta’addan da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun kashe wani babban Limami da wasu masu ibada uku yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban a lokacin da ‘yan ta’addan suka kai hari a kauyen Ngulde da ke karamar hukumar Askira-Uba a jihar Borno, kamar yadda majiyar Jaridar Yola 24 ta ruwaito.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa ‘yan ta’addan wadanda yawansu ya kai 20, sun kaddamar da harin ne a ranar Juma’a, inda suka bude wuta kan masallatan da suka kammala sallar Fajir a masallacin a cikin al’umma.

Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan sun yi awon gaba da dabbobi da kayan abinci tare da kona motoci biyu a yankin Ngulde da ke wani yanki na dajin Sambisa a jihar.

Da yake tsokaci kan harin, Kansila mai wakiltar Ngulde Ward a karamar hukumar Askira-Uba, Hon. Bilyaminu Umar, ya mika sakon ta’aziyya da jajantawa ga daukacin al’ummar mazabarsa kan harin da mayakan Boko Haram suka kai musu, wanda ya afku a ranar 2 ga Satumba, 2022.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN