Innalillahi An Gano Wani Coci Da Aka Garkame Almajirai 21 A Jos, Inda Aka Yi Kokarin Mayar Da Su Kiristoci Ta Karfin Tsiya
Jami’an DSS Sun Gano Wani Coci Da Aka Garkame Almajirai 21 A Garin Jos, Inda Aka Yi Kokarin Mayar Da Su Kiristoci Ta Karfin Tsiya
Hukumar tsaro ta DSS ta kai sumame wani gida da ke unguwar JMDB a yankin Tudun Wada da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, inda ta ceto wasu almajirai 21.
Da take tabbatar da lamarin, kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), ta shaida wa majiyarmu ta cewa mutanen da aka kubutar sun ce an kai su cocin ne ta karfin tsiya ana kokarin mayar da su addinin Kiristanci.
Babban Sakataren cocin ECWA, Rabaran Yunusa Nmadu, ya ce gidan da aka kai samamen na cocin ne, amma ba sa amfani da shi wajen canzawa mutanen addini da karfin tuwo.
DSS dai ta kai samamen ne ranar 14 ga watan Yunin 2022, inda ta ceto mutanen da ake zargin an kawo su Jos ne daga wata Jihar.
Kai samamen, a cewar Daraktan Agaji na JNI reshen Jihar ta Filato, kuma babban jami’in agaji na babban masallacin Juma’a na Jos, Danjuma Khalid, ya zo ne bayan daya daga cikin wadanda aka ceto din, Abdulrahman Usaini, wanda ya samu ya kubuto ya yi zargin cewa an killace su a gidan tsawon watanni takwas.
Khalid ya ce DSS ta kai samamen ne bayan rahoton na JNI.
Ya ce lokacin da aka kai biyu daga cikin mutanen da aka ceto – Abdulrahman Usaini da Nura Usama – din hedkwatar DSS da ke Jos, aka damka su ga JNI, kawun Abdulrahman da malaminsu sun kasance karkashin kulawar DSS har sai da aka gano danginsu.
Yadda aka kawo mu Jos daga Gombe – Abdulrahman
Abdulrahman, wanda dan asalin garin Azare ne a Jihar Bauchi, ya ce an kai shi garin Gombe ne don karatun Alkur’ani, inda daga nan ne aka kai shi cocin ta ECWA da ke Jos.
Ya ce a watan Oktoban 2021, yana kan hanyar dawowa daga makarantar da ke unguwar Pantami, inda wasu suka kira shi ya wanke musu mota kirar Toyota Camry, inda suka ce wa masu motar dare ya yi, amma aka danna su cikinta ta karfin tsiya.
“Sun kai mu cocin ECWA da ke Tumfure a Gombe, inda muka shafe mako uku a can. Bayan kwanakin, sai suka ce mana za a kai mu Jos.
“Wajen misalin karfe 4:00 na safiyar ranar, muka dauki hanyar tafiya Jos. Zuwa karfe 9:00 na safe mun kai hedkwatar cocin ECWA da ke Jos. Ban san Jos ba, wannan shi ne farkon zuwa na.
“Mun bukaci su mayar da mu Gombe saboda iyayenmu ba su san inda muke ba, amma suka ki.
“Bayan kwana daya suka mayar da mu wani gida da ke Tudun Wada, inda muka shafe wata takwas a ciki. A iya tsawon wannan lokacin, sun rika koya mana ilimin addinin Kiristanci. Su na ba mu abinci da dukkan abubuwan da muke bukata.
“Bayan mun shafe mako shida, sai aka kai mu cocin ECWA Good News da ke titin Ahmadu Bello do yin ibada a coci,” inji Abdulrahman.
Ya ce a ranar 13 ga watan Yunin 2022, ya sami damar tserewa bayan ya tsallake katangar gidan sannan ya gudu, yana neman agajin mutanen unguwar don ya sami komawa Azare a Jihar Bauchi.
Daga bisani aka kai shi wajen Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Kabeji reshen kasuwar Farin Gada, Adamu Alhaji Adamu, wanda shi ma dan asalin Azaren ne.
Ba ta karfin tsiya muka kai su gidan ba – Cocin ECWA
Sai dai da yake tsokaci a kan batun, Sakataren cocin ta ECWA, ya shaida wa Aminiya cewa wadanda aka ceto daga gidan ba ta karfin tsiya aka kai su ba, sabanin yadda suka yi ikirari.
Ya ce yana zargin cewa suna kokarin yin hakan ne don bata wa cocin suna, yana mai cewa cocinsu ba ta sauya wa mutane addini ta karfin tsiya.
Ya ce, “Babu kamshin gaskiya a labarinsu. ECWA kungiya ce ta kasa da kasa, kuma tana ayyukan alheri da dama, kama daga na lafiya da wa’azi da kuma koya wa mutane sana’o’i.
“Gidan da aka kama su ana amfani da shi ne wajen taimaka wa mutane ba tare da la’akari da kabila ko addini ba. Wajen kamar makaranta ne, kuma dole sai wani ya kawo ka kafin mu karbe ka.
“Ba ma karbar ’yan kasa da shekara 18. Muna karbar kudade kafin mu karbi mutum, muna koya musu sana’o’i na tsawon shekara daya, kafin mu yaye su,” inji Rabaran Yunusa.
Da aka tambaye su ko DSS ta fada wa cocin cewa za ta kai samame gidan, Sakataren na ECWA ya ce, “Su DSS ne ya kamata su amsa wannan tambayar. Watakila ba su san me ake yi a gidan ba, ka san kuma ba komai DSS za su fada maka ba.”