Innalillahi, Bayan Wuta ta kone Mai Jiki da Fuska Kalli Yadda Yakoma Wani Kala Abun Tausayi…
Qalu Innalillahi Wainna Ilaihi RajiUn Wani
Bawan Allah daya Gamuda Wata Kalar Cuta
Inda Jama’a Suke Tausaya Masa Duba’da
Irin Halinda Yake Ciki Abun Tausayi Gaskiya.
Wani Bawan Allah daya Kone a Jikinsa da
kuma Fuskar Sa Tabbas Yayi Matukar Baiwa
Jama’a Tausayi Inda Yasa Wasu Kuka
Saboda Halittun Sa Gabaki Daya Sun
Chanza Innalillahi. Ya Allah ka rufa Mana Asiri.
ALHAMDULILLAH: Daga Ƙarshe An Sayo Kayan Auren Ƴar Talla Mai Sallah Da Kuɗin Da Aka Tara Mata
A karshe dai gani tare da iyayen Hauwa’u da kayayyakin dauka saya musu daga gudummawa da bayin Allah suka bayar wanda jimillarsa ya kama naira dubu ɗari takwas da arba’in da bakwai da naira ɗari biyu da tamanin (N847,280.00).
Abubuwan Da muka saya sune kamar haka:-
1. Gado
2. Katifa
3. Complete set na kujeru
4. Labule (curtain)
5. Ledar tsakar ɗaki yadi goma
6. Kayan kitchen complete
7. Bed sheet
8. Turmi na daka
9. Food flask, flates, spoons da sauransu.
10. Buhun shinkafa guda 2 guda 1 za’a haɗa mata a cikin kayan gara, sauran guda 1 kuma iyayenta za suyi amfani da ita a gidansu.
Haka zalika tunda aure za’a yiwa Hauwa’u munyi mata tanadi na musamman domin dogaro Da kanta a gidan miji, mun saya mata kaya kamar haka:-
1. Keken Dɗnki
2. Awakai guda 4 Maza 2 Mata 2 Domin kiwo 3.Sai naira dubu Hamsin N50,000 (50k) za’a sayi itace ta dinga siyarwa a gida Duk dai saboda taci gaba da kulawa da kanta.
Itama mahaifiyarta an bata dubu Hamsin (50k) Domin ta ƙara jarinta na sana’ar awara da take yi.
A bangaren mahaifinta kuwa shima ya rabauta da naira dubu hamsin (50k) domin yaci gaba Da sana’arsa ta fruits da ya daina yi sakamakon rashin jari. A farko munyi niyyar bashi dubu 100 ne amman sakamakon mun fahimci gidansa yana buƙatar ƴan gyare-gyare sai muka bashi dubu hamsin ya ƙara jarin, sauran dubu hamsin ɗin da sauran kuɗin da ya rage za muyi amfani dasu wajen gyara musu banɗaki, ɗakin girki, rijiya da wani ɓangare na katangar jikin gidan data rushe a gidan nasu Hauwa’u.
Total kuɗin furnitures, Katifa, ledar tsakar ɗaki N346,500.
Total kuɗin keken dinki, Awakai, shinkafa buhu 2 labulaye Da Sauransu N210,500.
Transport cost N22,000.
Mun cika N43,000 Mun sayi sauran kayan Kitchen saboda akwai wata baiwar Allah data bamu wasu daga ciki.
Total kuɗin da aka vawa Hauwa’u da iyayenta da sauran 50k Da za’ayi musu gyara ya kama dubu ɗari takwas da goma N832,000.00
847,280-822,000 = 25,280.00
Kuɗin da ya rage 25,280.00 sune zamu hada da sauran dubun hamsin ɗin da muka ware domin gyara wani ɓangare na cikin gidansu kamar yadda nayi bayani a sama.
Mun ja hankalin saurayinta wanda shine zata Aura da yayi ƙokari ya riƙe Hauwa’u da Amana, kuma ya ƙara tsaya mata taci gaba da zuwa makarantar Islamiyyar data saba zuwa tunda matan Aure ma suna zuwa.
A karshe ina jinjina da godiya ta musamman ga waɗanda suka bada gudunmowa ta kuɗi, wasu daga cikin kayan kitchen, shawarwari da addu’a, Allah ya sakawa kowa da alkhairi, Allah ya biya mana dukkan buƙatunmu na alkhairi.
DAGA: Abdulmutallib Hamza Kibiya