Innalillahi. Bidiyon Yadda Aka Ciro Gawarwakin Wasu Mata Hudu Da Suka Gamu Da Ajalin Su A Ballewar Jirgin Ruwa A Jigawa
Rundunar yan sandan ta Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wata yarinya yar wata bakwai da wasu mata hudu bayan da kwalekwalen su ta kife a karamar hukumar Guri.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar DSP Lawan Shiisu, ya tabbatar da afkuwar lamarin a Dutse babban birnin jihar.
Ya ce lamarin dai ya faru ne da yammacin jiya Talata, inda yarinyar da kuma matan suka shiga kwale-kwale daga Nguru a jihar Yobe zuwa kauyen Adiyani na karamar hukumar Guri na jihar ta Jigawa.
Abin takaicin itace kwale-kwalen ya kife suna daf da isa inda za su je. Amma matukin kwale-kwalen ya samu damar fita da ransa, yayin da su kuma fasinjojin suka nutse, a cewar Shiisu.
Ya ce lokacin da lamarin ya faru, direbobi da ke yankin sun yi kokarin ceto fasinjojin abin bai yu ba, sai dai gano gawarwakinsu da aka yi.