Labaran duniya

Innalillahi jarumin Kannywood yanke jiki ya Fadi yana tsaka da tirka rawa da wasu Yan mata a gidan gala

A KARON farko, fitaccen jarumin finafinai Hausa, Tahir Mohammed Fagge, ya ɓara kan dalilin da ya sa ya yi rawa tare da wasu matasan mata a bainar jama’a a wajen wasan gala.

Tun a farkon 2020 ne aka fara yaɗa bidiyon rawa da waƙar da Tahir ya yi tare da matan a wani wasan gala, inda aka gan su su na bin wata waƙar Hamisu Breaker Ɗorayi, to amma bidiyon bai haifar da surutai ba sai a bana lokacin da aka ƙara wallafa shi a soshiyal midiya, musamman a TikTok da YouTube.
Da yawa waɗanda su ka kalli bidiyon sun ce jarumin bai kyauta ba da aka gan shi ya na rawa da yaran mata sa’annin jikokin sa.

Sai dai a tattaunawar da ya yi mujallar Fim kwanan nan, Tahir Fagge ya kare kan sa tare da yin kakkausan martani ga masu cewa abin da ya yi bai kyauta ba.
Ya faɗa wa mujallar cewa ya na jin duk maganganun da ake yi a ciki da wajen industiri dangane da bodiyon.

Daga nan ya ɗauko bayanin yadda abin ya faru tun daga tushe, kamar haka: “Lokacin da abin ya faru, ina kwance ne a gida, ba ni da lafiya; na samu matsalar cutar shanyewar ɓarin jiki, har ya zama ba zan iya tafiya mai tsayi ba a lokacin har sai na zauna na huta. Kuma ba ni da kuɗin da zan je asibiti, kuma ina neman kuɗi N260,000 wanda da shi ne za a ɗauki hoton zuciya ta, za a ɗauki hoton ƙirji na da yi mani magani.

Yaran nan su ka zo har gida su ka same ni, su ka ce ko da ba zan yi rawa ba, su na so na je wajen na zauna a matsayi na na babban baƙo. Kuma a nan su ka ɗauki kuɗi N160,000 su ka ba ni. Ka ga saura N100,000 kenan.

Source: Fimmagazine.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN