Labaran duniya

Innalillahi Kalli yadda Wani Manomi Yayiwa Wata Mata kisan gilla kamar yadda ake yankan Rago

Wani Manomi Yayiwa Wata Mata kisan gilla ta hanyar yankan Rago a Jihar Neja.

Daga Hassana Magaji.

“Ana Zargin Wani Manomi Mai Suna Tafiya da Yiwa Wata Mata Mai Suna Hajjo Yankan Rago, Wanda Yayi Sanadiyyar Mutuwar ta Nan Take.

Lamarin dai Ya Aukune a Wani Gari da Ake kira Magono Kauyen Gulbin Boka Dake Karamar Hukumar Bangi a Jihar Neja,Yayin Bincike Angano Cewar Mutumin Ya Yankata ne Sanadiyyar Shiga Gonan Gyadan shi da Dabbobinta Sukayi Inda Sukaci Wani Sashi na Gyadan daya Shuka.

Lamarin dai Ya Haifar da Cece Kuce Tsakanin ‘Yan Sanda Da Mutanen da Lamarin Ya Shafa Inda Dakyar da Sudin Goshi Suka Amince da Bayar da Gawan Hajjon Domin a Sallaci Gawar nata.

“Har Yanxun dai ‘Yan Uwan Wanda Ake Zargi da Aikata Kisan Sunyi Dafifi a Harabar Ofishin ‘Yan Sandan dake Gulbin Boka Inda Suke Neman Abasu Belin Wanda ake Zargin, Yayinda Rundunar ‘Yan Sandan Sukayi Watsi da Bukatar ta su.

“Tuni Angudanar da Jana’izar Marigayiyar Kamar Yadda Addinin Musulunci Ta Tanada,Sedai A dayan Bangaren ‘Yan Uwanta Nakira da Masu Ruwa da Tsaki dasu Gaggauta bi masu Hakkin Wannan Aika Aika.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN