Innalillahi wa inna ilaihi rajiun ashe maganar da ake ta masu satar majalisar dinkin dunia gaskiyane
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun ashe maganar da ake ta masu satar mazakutar gaskiya ne 😢
Kuyi haquri ba iskanci bane wallahy da da inajin abun ban yadda bane se yanzu naga wannan videon shiyasa nake bawa mutane shawara a kiyaye yawan gaisuwa a gun taro da wanda baaa saniba
RAHOTO: Ana Cigaba Da Fuskantar Barazanar Satar Mazakuta A Yankin Abuja Da Kewayen Marararraba/Nyaya
..An konawa wani mutum motar sama da milyan 30 a Mararraba/Nyaya bayan an zarge shi da satar al’aura
Daga Aliyu Ahmad
Jita-jitar satar àĺ’àùŕà na cigaba da yaduwa a yankunan babban birnin tarayya Abuja da kewaye, inda kusan a ‘yan kwanakin nan kullum sai an samu labarin an sacewa wani gaba, walau a cikin kwaryar Abuja ko kuma a yankunan dake makwabtaka da ita.
Binciken jaridar Rariya ta gano cewa lamarin ya kara kamari ne a cikin makon da ya gabata zuwa karshensa, inda a tsakanin Mararraba an samu aukuwar lamarin har sau wajen hudu. Haka ma a yankin AYA dake Abuja an samu aukuwar hakan.
Ko a safiyar jiya Lahadi, an yi guje-guje akan titin kasuwar ‘yan lemo dake Mararraba kusa da mayanka (kwata), sakamakon tarwatsa jama’a da jami’an tsaro suka yi da barkonon tsohuwa domin ceto wani da mafusata suka rufe shi da duka bisa zargin sa da satar àĺ’àùŕà.
Sannan da yammacin jiya Lahadin an sake samun aukuwar lamari makamancin haka a yankin Sharp Corner, inda shi ma wannan mutumin da ake zargi da sace mazakutar ya ci na jaki a wajen jama’a.
Haka ma a ranar Asabar an kona motar wani ta kimanin naira milyan 30, bayan wasu da ya ragewa hanya suka yi kururuwar cewa ya kwashe musu mazakuta, inda nan take jama’a suka rufe shi da duka har ta kai ga an bankawa motarsa wuta.
Haka ma a wani ofishin ‘yan sanda dake Abuja an samu korafi daban-daban na mutanen da aka sacewa gaba har da mata.
Saidai duk da cewa ana ta samun labarin aukuwar wannan lamari, wasu suna ganin ba gaskiya ba ne, kawai sharri ake yi wa mutane, har ta kai an rufe su da duka a illata su, wanda kuma idan hukuma ba ta tashi tsaye ba za’a samu babbar matsala.