Labaran duniya

Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un yadda Uwa da Diya Suka Rasa Ransu Sakamakon Hadarin Mota

Anyi Jana’izar Uwa Da Ɗiya Ƴan Garin Dutsin-ma Da Suka Rasu Sakamakon Haɗarin Mota.

Daga Zaharadden Surajo Abbass.

Muna cikin jimami sanar da ku rasuwar daya daga cikin mabiya wannan Jarida mai albarka Hajiya Wasila Amadu wacce take amfani da sunan ( Umm Sajjad) sun rasu ita da mahaifiyarta a kan hanyarsu ta dawowa daga Jahar Jigawa wajen wata ta’aziyya.

Lamarin da ya faru bayan sallah Mangariba wajen Kauyan Sha’iskawa hanyar Kankiya, inda nan take ita ta mahaifiyarta suka ce ga Garinku nan, wasu daga cikin motar sun samu karaya a kafa shi kuma direban ya bugu a gurare daban daban na jikinsa

Wakilinmu ya halarci jana’izarsu a Garin na Dutsanma tare da kawo kadan daga cikin nasihar da wani Malami ya gabatar kafin yin addu’a, ya fara cewa ina kiran Al’umma “akan kowama ga Allah yana mai cewa wadannan bayin Allah lafiyarsu kalau jiya amma yau gamu mun rakosu gidansu na gaskiya,wallahi mun sani watarana mu za’a kawo ko kai ko ni, wallahi kowa ya an kawo shi nan ko ya shirya ko bai shirya ba.

Idan maganar shiri ake yi wadannan bayin Alah basu zuwa inda zasu tarar da aljalinsu, amma babu yadda suka Iya gashi yanzu zamu tafi mu barsu”.

Ya cigaba da cewa nasan hajiya Wasila tare muka Makaranta bata da Abokin gardama balle fada, duk inda zaka kwatatanta Mutum wajen kirki da Mu’amula to ta kai, muna fatan Allah Ya gafarta masu, mu sani kuma mu kiyaye wannan yana tare gamu, kuma daga mu sai aikinmu kamar yadda makiya da masoyan wadannan bayin Allah basu kara ganinsu har abada.

Daga karshe karshe Al’umma ku sani ba’a daga muryar cikin makabarta, amma yanzu abunda ya samemu shi ne zaka ga wadanda aka yi wa rasuwa kadai ke cikin juyayi sauran Mutane suna ta hira da sakin baki, ku sani nan gurin addu’a ne da tuna Allah.

Muna mika sakwan ta’aziyyarmu ga daukacin Al’ummar Musulmi baki daya da Al’ummar Garin katsina, iyalan Marigayi Alh Amadu Mai Biredi Dutsanma Nura Amadu Abba Ahmed Planner Jamilu Amadu Murtala.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN