Labaran Kannywood
Innalillahi Wainna ilaihirrajiun Allah Yayiwa Mahaifiyar Jarumi Tijjani Faraga rasuwa
Innalillahi Wainna ilaihirrajiun Allah Yayiwa Mahaifiyar Jarumi Tijjani Faraga rasuwa
Fim Magazine: Jarumi a Kannywood, Malam Tijjani Faraga, ya bayyana irin halin kaɗuwa da ya shiga saboda rashin mahaifiyar sa da ya yi, wato Hajiya Rabi’atu Usman.
Da ya ke tattaunawa da mujallar Fim kwana uku bayan rasuwar mahaifiyar tasa, Malam Tijjani ya ce: “Gaskiya ban taɓa rashin wani ɗan’adam da ya kai mahaifiya ta ba. Tun lokacin da ta rasu a rikice na ke.
Marigayiyar dai ita ce babbar yaya ga Babban Limamin garin Jos, Sheikh Lawal Adam. Allah Yaji Kanta da rahama idan tamu tazo yasa mu cika da kyau da iman ameen