Jami’an Ƴan Sanda A Kano Sun Kama Jarumin Finafinan Hausa, Malam Ali Kwana Casa’in
Jami’an Ƴan Sanda A Kano Sun Kama Jarumin Finafinan Hausa, Malam Ali Kwana Casa’in
Kamun nasa dai ya biyo bayan umarnin da kotu ta yi wa A.I.G na shiyyar zone one bayan shigar da ƙarar bata suna da Marubuci Imam Aliyu Indabawa ya yi a kansa.
Indabawa ya shigar da ƙarar Jarumi Malam Ali Kwana Casain yana iƙrarin ya ɓata masa suna ta hanyar shirya karairayi.
A ƙarshen shekarar 2022 an ji muryar Malam Ali a kafafen watsa labarai yana cewa Indabawa ya dinga kiransa a waya yana yi masa barazana kan ko ya ba shi kuɗi ko ya ɓata masa suna, da ya ƙi ya ba shi kuɗin shi ne ya yi masa sharri, Malam Ali ya ce duk yana da recording ɗin kiran da kuma sauran hujjoji.
To sai dai Indabawa ya musanta wannan magana yana mai cewa sharri da batanci Malam Ali ya yi masa, kuma ya maka shi a kotu domin ya tabbatar da maganganunsa.
A cewar Indabawa” Malam Ali ya kai ni wurin ƴan sanda yana iƙrarin na yi masa barazanar ya ba ni kuɗi ko na yi masa ƙazafi, wai da ya ƙi ya ba ni shi ne na yi masa sharri, daga wurin ƴan’sanda muka tafi kotu amma ya kasa kawo hujjar maganganunsa ƙarshe ya janye ƙarar.
Tun a wancan lokacin ban sami hurumin shigar da shi kara a dokance ba sai yanzu.”
Daga ƙarshe dai an bayar da belin Jarumin inda ake ci gaba da zurfafa bincike.
Daga Abdulrashid Abdullahi Kano