Labaran duniya

Jami’an Tsaron Saudiyya Sun Cafke Mutumin Da Ya Sadaukar Da Umararsa Ga Sarauniyar Ingila Elizabeth

Jami’an Tsaron Saudiyya Sun Cafke Mutumin Da Ya Sadaukar Da Umararsa Ga Sarauniyar Ingila Elizabeth

Rahotanni daga ƙasar Saudiyya sun bayyana cewar jami’an tsaron ƙasar sun kama wani mutum da ya je musamman dan yin Umara ga Sarauniya Elizabeth.

Mutumin ɗan Yemen ne kuma ya saki bidiyonsa a ranar Litinin a babban masallacin Makka na Ka’aba wanda aka haramta wa waɗanda ba musulmai ba zuwa.

A bidiyon ya riƙe wata takarda wacce aka rubuta:

“Mu na fatan Ubangiji ya amincewa Sarauniya Elizabeth II shiga Aljanna, ya kuma sanyata cikin amintattunsa.”

Bidiyon ya yadu a shafukan ma’abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani da ke Saudiyya, inda mutane da dama su ka bukaci a kama shi.

Tuni dai hukumomin ƙasar suka bayya cewar an kama shi, kuma an gurfanar da shi don yi masa hukunci daidai da abin da ya aikata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN