Labaran Kannywood

Jaruma Zee Pretty ta Fashe da Kuka bayan taga irin Wannan Kyautar da aka bata a birthday dinta

Jaruma Zee Pretty ta Fashe da Kuka bayan taga irin Wannan Kyautar da aka bata a birthday dinta

Fitacciyar Jaruma Masana’antar Kannywood wacce akafi sani da Zee pretty ta fashe da hawaye bayan ganin irin tarin kyaututtka da abokan arziki da yan uwa suka kawo mata.

Kamar dai yadda wasu suka sani a shekaran jiya ne jarumar tayi bikin murna Zagayowar Ranar Haihuwar ta harma jarumai da dama suka wallafa hotunan ta domin tayata murna.

Wanda a karshe kuma aka bita da kyaututtka da suka saka ta zubda hawaye, kalli cikakken vedion anan

Na Shiga Harkar Fim Domin Fadakarwa Ne~ Cewar Jaruma Zee Pretty

Fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Zulaihat Ibrahim wacce aka fi sani da Zpreety, ta bayyana cewa, kokarin ta fadakar da jama’a ne ya sa ta shigo harkar fim, don haka ta zo harkar ne, domin ta isar da sako domin fahimtar da mutane.

Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin jaridar Dimukaradiyya, inda ya ke yi mata tambaya dangane da dalilin shigowar ta masana’antar.

Jarumar ta bayyana cewar “Na dauka a raina na shiga harkar fim ne, domin na isar da wani sako mutane su fahimta kuma su karu, don haka ma na ke son duk masu son shigowa harkar fim kada mutum ya shigo da tunanin su yi suna, don ko ba ka bukaci ka yi sunan ba idan Ka yi abu abin da ya dace, to za ka samu, don haka tsare mutunci da sanin ya kamata shi ne zai sa ka samu matsayin da ka ke nema. ” Inji ta.

Da muka tambaye ta maganar aure kuwa cewa ta yi.

” Ni ba na shigo harkar fim ba ne da nufin babu aure a gabana ba, duk lokacin da Allah ya kawo mini wanda muka fahimci juna da shi, za mu yi aure da shi, domin shi aure sunna ce ta Manzon Allah, da iyayen mu ba su yi aure ba, da ba za su same mu ba, kuma su ma burin su ne su ga muna yi auren. ” a cewar ta.

A karshe ta yi kira ga mata yan fim da cewar, ya kamata su rinka kula da wanda zai zo wajen su da sunan zai aure su, domin akwai yan yaudara sosai, inda ta ce, “Mata a nutsu a rinka kulawa” In ji Zpreety.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN