Kannywood
Jawabi akan halacin crypto da mining daga bakin malamai mabambanta
Cryptocurrency: Mene ne matsayin addinin Musulunci kan amfani da kudin intanet?
Yayin da sabon kudin intanet Cryptocurrency ke ƙara shahara a duniya, wasu malaman addinin Musuluncin sun ce bai halatta a yi amfani da kudin na Cryptocurrency ba.
To sai dai wani malamin addinin Musulunci a Abuja Najeriya, Ustaz Husayni Zakariyya, wanda ya yi digiri na biyu kuma yake karatun digiri na uku kan matsayin addinin Musulunci dangane da amfani da kudin intanet wato Cryptocurrency, ya ce a bincikensa ya gano cewa halal ne amfani da sabon kudin.