Kai Tsaye Daga Wajen Shari’ar Fatima Wacce Aka Yankewa Kafa Bayan An Bigeta da Mota
An Shiga Kotu A Yau Litinin Domin Sauraren Shari’ar Fatima Wacce Aka Yankewa Kafa Sakamakon Buge Ta Da Mota
…saidai ‘yan uwan Fatima sun soma zargin ba za a yi musu adalci ba saboda yaron dan masu hali ne
A yau ne aka shiga kotu wajen zaman yanke hukunci ga wanda ya yi sanadiyar buge Fatima da mota, amma Alkalin kotun bai samu zuwa zaman na yau ba, saidai kuma an samu hargitsi wanda ya yi sanadiyar jami’an tsaro suka hana ‘yan jarida da sauran al’umma daukar hoto ko bidiyo a wurin.
A dalilin hakan ne wasu a bangaren Fatima suna zargin kotun da ba za ta iya musu adalci akan wanda ya yi sanadiyar buge `yar su ba saboda bangaren iyayen yaron masu kuɗi ne sannan kamar dai ana so a canza labarin.
Ya kamata jama’a ku fito domin mu nemi ‘yanci ga Fatima