Kalli Jerin Manyan Malaman Najeriya da suka raigamu gidan gaskiya
Allah Sarki Rayuwa 😭 Kalli Jerin Manyan Malaman Najeriya da suka raigamu gidan gaskiya da Ranar da Allah ya Karbi Rayuwarsu, Muna Fatan Allah ya jikansu da Rahama 🙏🙏
SHEIK JAFAR MAHMUD ADAM:
An kashe Sheikh Ja’afar ne a cikin masallacinsa a lokacin sallar Subh a birnin Kano a watan Afrilun 2007. An dai raba ra’ayoyi a wancan lokaci dangane da wadanda suka aikata wannan aika-aika. Yayin da wasu ke cewa kungiyar Boko Haram ce ta kashe Shehin Malamin, wasu kuma na cewa Malam Shekarau, gwamnan Kano a lokacin, shi ne ya dauki alhakinsa saboda malamin na daya daga cikin manyan masu sukarsa.
A duniyar muslunci, ko a tarihi, ba’a taɓa malami bahaushe irin Sheikh Jafar Mahmud Adam ba.
Rahimahullah 🥲
1. Kwarewa a tafsirin alkur’ani maigirma
2. Ilimin tauhidi
3. Gwagwarmaya
4. Uslubin da’awa
5. Malamin da bai ɗauke duniya komai ba, kuma kudi ko jindadin duniya ba nashi bane.
Ina kyautata zaton sheikh jafar mahmud adam da’awar gaskiya yakeyi kuma domin neman yardar Allah
Baya fada da malami ɗan uwansa ko dalibinsa, shi babban burinsa al’umma su fahimce addinin gaskiya.
Allah ya gafarta maka malam😭
SHEIK ALBANI ZARIYA:
Allah ya karbi rayuwar Masoyinsa na kwarai, Malam Albani zaria ne a February 2014.
Kamar yadda Malam Bello Nakaka ya bayyana, harbe-harben bindiga da suka lullube motar da Sheikh Albani ke tukawa ya yi kamar ana ruwan sama. Ya bayyana tserewar tasa a matsayin abin al’ajabi domin manufar ‘yan bindigar ita ce kashe dukkan mutanen da ke cikin motar. Har ya zuwa yanzu, Nakaka ya kasa fahimtar kwarewar masu kisan, kwanaki bayan kisan gillar da aka yi wa malamin.
A cewar Nakaka, dalibin malamin marigayin, mutanen da suka kashe Sheikh Albani sun hau babur ne kuma suna sanye da kwat da takalma, kamar yadda ‘yan wasan kwaikwayo ke taka rawar kashe-kashe a fina-finan kasashen waje.
SHEIK ABUBAKAR GERO ARGUNGU:
Allah ya yi wa wani babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Gero Argungu rasuwa a ranar Laraba a garin Birnin Kebbi na jihar Kebbi, bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau ya bayyana rasuwar Argungu.
Sheikh Abubakar Gero Argungu ya samu karramawa sosai a tsakanin al’ummar musulmi saboda irin gudunmawar da yake bayarwa ga addinin musulunci da kuma matsayinsa na jagora.
SHEIK ABUBAKAR MAHMUD GUMI:
Abubakar Mahmud Gumi (7 Nuwamba 1924 – 11 Satumba 1992) malamin addinin Musulunci ne na Najeriya kuma Grand Khadi na yankin Arewacin Najeriya (1962 – 1967), matsayin da ya sanya ya zama babban jigo wajen tafsirin tsarin shari’a. a yankin.
Allah ya karbi rayuwar fitaccen jarumin addinin Musuluncinnan a shekarar 1992.
SHEIK ADAMU MAI GORA:
Allah ya yi wa Sheikh Adamu Aliyu Maigora Kaduna, Babban mai gabatarwa a mambarin Jibwis na kasa (National M.C) rasuwa.
Kungiyar Jibwis ta yi babban rashin da zai yi wahala a iya cike gurbinsa.
Sheikh Maigora ya karar da rayuwarsa a cikin dawainiyar Musulunci.
Tarihin kungiyar Izala ba zai manta da Maigora ba.
SHEIK YUSUF ALI:
Sheikh Yusuf Ali Ya Rasú: Allah ya yiwa Babban Malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Yusuf Ali rasuwa.
Sheikh Yusuf Ali was a Nigerian Kano Islamic cleric. He was a member of the Islamic Sufi group known as the Tijaniyyah in Nigeria. Ali was also an Upper Shari’a Court judge, and director of the court in 1974.