Kalli yadda aka Kama Yan Boko Haram a gidan Atiku suna shirin tada Bam
Kalli yadda aka Kama Yan Boko Haram a gidan Atiku suna shirin tada Bam.
Atiku Abubakar ya Salleke Rijiya ta baya!
Yanzu Yanzu an Kama Yan Bindiga 2 da Ake Zargin ‘Yan Boko Haram ne na Shirin ta da Bam a Gidan Atiku.
KALLI BIDIYON ANAN 👇
PLAY ▶️
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da cafke wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne a yunkurin su kai mummunan hari gidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a Yola, jihar Adamawa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, Suleiman Nguroje, ya shaida wa jaridar SaharaReporters a safiyar yau Litinin cewa, a ranar Lahadi jiya ne jami’an rundunar suka kama wasu ‘yan ta’adda biyu da ake zargin su da hannu wajen shirin tada Bam a gidan Atiku Abubakar inda nan take aka mika su ga sojoji domin ci gaba da bincike.
“Eh, an kama wani Jibrilla Mohammed a gidan tsohon mataimakin shugaban kasa da ke Yola, kuma a lokacin da muke yi masa tambayoyi mun samu nasarar cafke dan uwansa da suke da hannu a cikin wannan shiri.
“Mun mika su ga sojoji, domin su bincike su sosai kan laifin ta’addanci da muka same su dashi,” inji shi.
Atiku, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa a 2023, a halin yanzu yana kalubalantar zaben shugaban kasa Bola Tinubu a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa; bayan da ya sha kaye a zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu