Kalli yadda aka Kori Sojojin Da Suka Kashe Sheik Goni Aisami A Jihar Yobe Daga Aiki
An Kori Sojojin Da Suka Kashe Sheik Goni Aisami A Jihar Yobe Daga Aiki
Rundinar sojin Nijeriya ta kori sojoji guda biyu wadanda ‘yan sanda suka kama da laifin aikata kisan kai da fashi da makami.
Sune sojojin da suka harbe babban Malamin Musulunci a jihar Yobe Sheikh Muhammad Goni Aisami tare da yunkurin sace motar Malamin.
Sojojin masu mukamin Lance Corporals wato Lance Corporal John Gabriel da Lance Corporal Gideon Adamu, amma kafin a koresu daga aiki sai da aka rege musu matsayi zuwa kuratan Sojoji wato Private.
Laftanar Kanar Ibrahim Abdullahi Osabo shine Mukaddashin Kwamandan Recce Battalion rundina ta 241 dake da sansani a garin Nguru jihar Yobe inda sojojin suke aiki ya gabatar da korarrun sojojin, sannan ya mikasu wa ‘yan sanda domin a gurfanar da su a Kotu.