Kashi 70 na yan Mata suna Adana Bidiyon Tsiraicinsu a Cikin wayoyinsu
NAZARI: Yawan Tsinuwa Da La’anta Ya Taimaka Wajen Lalacewar Safara’u
Sau da yawa mutane ne suke daɗa zama silar shigar wasu mutanen halaka, idan mutum yana aikata sabo basa tunanin su fadakar da shi, kullum tunaninsu ya za a yi su muzanta shi, hakan kuma ke sakawa mai aikata laifin ya cigaba abinsa.
Idan ka saurari hirar da BBC-Hausa su ka yi Safara’u Kwana Casa’in a yau za ka tabbatar da haka.
A lokacin da bidiyon tsiraicinta ya bayyana babu irin cin zarafi da kalaman tsinuwa da la’anta da mutane ba su yi mata ba wanda hakan ya zama silar ƙara shigarta cikin mummunar rayuwa.
Mutane suna mantawa wanne hali a gaba za su tsinci kawunansu ko ƴaƴansu ko ƴan uwansu domin babu wanda ya fi ƙarfin Allah Ya jarrabe shi a rayuwa duk nagartarsa da ingancinsa.
Sannan mutanenmu yanzu musamman a social media sun fi zaƙewa akan hango laifuffukan wasu alhali su ma idan aka yi bincike Allah ne kaɗai Ya san irin taɓargazar da su ke aikatawa ɓoye.
Daga Mutawakkil Gambo Doko