Labaran Kannywood

KE DUNIYA: kalli yadda Aka kama wanda yasace Makarar Ɗaukar Gawa A Wani Masallaci A Kaduna

KE DUNIYA: An Sace Makarar Ɗaukar Gawa A Wani Masallaci A Kaduna

Rahotanni sun tabbatar da cewar an sace Makara a Masallacin Hayin-Banki dake yan-shinkafa dake ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa (Kaduna North) dake Jihar Kaduna.

Masu halartar Masallacin sun bayyana cewar Limamin Masallacin ne yake bayyana hakan a lokacin gabatar da khuɗuba a ranar Juma’ar da ta gabata.

Rahotannin bayan fage sun gasgata cewar Makarar da aka sace ta ƙarfe ce, har ma ana danganta batun da masu siyar da ƙarfe a kan sikeli a cikin unguwanni.

Limamin Masallacin Juma’an, yayi tsokaci tare da jan hankali kan satar kayan mutane musamman a Masallatan unguwanni.

Daga Shu’aibu Abdullahi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Tallafin Ramadan N75,000 Daga Gwamnati

X
KALLI BIDIYON ANAN