Labaran Kannywood

Kudaina zargin Yar fim don aurenta ya mutu Inji Jaruma Mansura Isah

Kudaina zargin ‘Yar fim don aurenta ya mutu Inji Jaruma Mansura Isah

Daga Barrista Nuraddeen Isma’eel

“Ina da wata kawa “Yar fim ce, bayan tayi aure sai mijinta zai kara wani auren daban, a nan kuma gefe mijinnata bashi da inda zai sakata sai yace zai kawota gidan da ita kawar tawa take, kawai da rana tsaka sai mijinnata yace ya saketa, nan take kawar tawa ta zube kasa tana kuka gwiwoyinta kasa tana bashi hakuri yace ai shifa ya saketa hakanan Suddan wallahi.”

“Tshohuwar jarumar ta cigaba da cewa, wallahi kuma ita kawar tawa ‘Yar fim din ba abinda tayi masa, kawai Daga karshe sai yace taje kano ta cigaba da yin fim dinta, wani lokaci na ziyarci shafinta a fesbuk haka naga jama’a yadda suketa zaginta ai bata son zaman aure, a nan ko jama’a basu mata adalciba saboda basusan me yasa ta rabu da mijintaba, sai kaji mutane suna cewa wai ai ‘Yan fim basu son zaman aure wannan ba gaskiyabane wallahi, akwai ‘Yan fim din da tunda sukayi aure baka kara jin duriyarsu ba a masana’antar shirya wasan Hausa suna can suna ibadansu su wadannan kaddararsu kenan.” 

“Mansura Isah a cikin fai-fan bidiyonnata da jaridar Aminiya tacigaba da cewa, suna samun kulawa a gidajen zaman aurensu, kama daga ci sha sutura na alfarma, gida kudi mota Alhamdulilah, toh’ me yawuce haka ga duk mace taga kanta a haka, amma akwai abinda zai hadasu da miji Wanda Ku jama’a Baku saniba, a’a kawai da ‘Yar fim tafito gidan miji zaku fara zaginta ai daman haka tafiso tafito tacigaba da karuwanci, ya kamata mutane su mana adalci, mutuwar aure ba akan ‘Yan fim kawai aka faraba, kuma duk mace bawacce zataso ace tayi aure daga baya tafito daga gidan mijinta.”  

“A nan kuma hartake bada misali cewa, da za’aji labari mace saboda da damuwa a gidan mijinta har ya kai ga ta fadi, zaka ji ana cewa! Me yasa bata fitoba ? Matastar ko za’ace haka don mace na samun damuwa har yafito fili, banga ko dalilin da zaisa Abu ya faru a tsakanin mata da miji har ta kai ga tafito musamman ‘Yar fim kuma jama’a su fara cewa! Ai tafito karuwacine wannan rashin adalcine karara da ake mana.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN