Labaran duniya

Kungiyar ASUU Bata Janye Yajin Aiki Ba

Ainahin Sahihin Zance Game Da Batun Janye Yajin Aikin Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU

…Har zuwa yanzu ASUU bata janye yajin aikin ta ba.

Rubutawa da bincikawa ✍️
Comr Abba Sani Pantami

Kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa, nan kusa kadan kungiyar malaman jami’a za ta koma bakin aiki bayan shiga tsakani da yayi.

Kakakin na majalisa ya bayyana hakan ne a ganawarsa da shugaban ASUU, Fafesa Emmanuel Osodeke da sauran kusoshin kungiyar da yammacin jiya Litinin 10 ga watan Oktoba.

A cewarsa yau Talata Shugaba Buhari zai bayyana yadda zaman sulhun ya gudana.

Shugaban ASUU na kasa ya kara da cewa: “A karon farko, mun ga haske a karshen lamarin.”

Ga abubuwa 3 da ASUU zata gudanar kafun sanarwar janye yajin aiki.

1, A yau Talata, 11 ga Oktoba 2022 Shugabannin yankuna na ASUU zasu tattauna kan shawarin Kakakin Majalisa Gbajabiamila ya baiwa Shugaba Buhari don kawo karshen yajin aikin.

2, A gobe Laraba 12 ga Oktoba 2022 bayan jawabin da ake sa ran Shugaba Buhari zai yi yau (Talata), ASUU zata gana da daukacin mambobinta don yanke shawara kan kalaman Buhari da kuma shawara ko sun yarda.

3, A Ranar Alhamis, 13 ga Oktoba 2022 Majalisar zartaswar ASUU zata zauna don duba shawarin mambobinta da kuma yanke shawarar karshe.

Idan komai ya daidaita, zuwa ranar Alhamis da Dare ko kuma wayewar garin Juma’a za’a janye daga yajin aikin baki daya.

Muna fatan Allah ya tabbatar mana da mafi Alkhairi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN