Labaran duniya

labaran duniya – Kalli yadda aka Kama Malaman Coci suna siyar da Yara Kanana Akan Naira 50,000

An kama malaman coci a Jihar Ribas da yara 15, tace dubu 50,000 take Sayan yaro daya

Daga Hajiya Mariya Azare

Wata malaman coci ta shiga hannu yayin da ake zargin tana fataucin kananan yara a jihan Ribas.

Rundunan ‘yan sanda sunyi bayanin yanda suka kamo ta da kuma yadda aka kame wasu mutane da dama.

Malaman mai suna Maureen Wachinwu, tace takan sayi yara akan dubu hamsin 50, 000 dubu 60, 000 ko dubu 100, 000 daga hannun wani mutum dake kawo matasu.

Bayan samun bayanan sirri, ‘yan sandan sun kama maureen a gidanta dake aluu ta karaman hukuman ikwerre a jahan Ribas, tare da ceto yara kanana har 15 daga gidanta.

Kwamishinan ‘yan sandan jahan friday Eboka, ya bayyana cewa yaran da aka gano a hannun matan ‘yan shekaru 7 zuwa 9 ne, inda ya kara da cewa za’a gurfanan da ita bayan gama cikekken bincike.

Eboka yace binciken farko na yan sanda ya nuna cewa andakko yaran ne daga sassa daban daban na jahohin kudu maso kudu a nijeriya, kuma dagaske sayan su tayi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN