Labaran duniya

Allah sarki Kalli Aka tsinci Gawar Mutumin Daya Shekara Hudu a Dakinsa Kulle a Ibadan

An tsinci Gawar Mutumin Daya Shekara Hudu a Dakinsa Kulle a Ibadan

Daga Rafi’atu Mustapha Katsina

Ma zauna na cikin zullumi tun bayan da aka samu kwarangwal din mutum a cikin dakinsa, bayan shekaru hudu a apete dake ibadan.

Ana tunanin cewa kwarangwal din gawar (wanda ba a bayyana ba) An samu rahoton tane daga makwabta shekaru hudu da suka wuce ayayin da yake zuwa daga ibadan zuwa Port Harcourt,a garin river inda anan yake zaune a wannan lokacin.

Har a lokacin hada wannan rahoton ba a samu wani bayani game da abunda ya haddasa wannan kwarangwal din gawar ba.

Ma zauna unguwar sun shaida wa manema labarai cewa,babu wani dan unguwar daya sanda faruwar lamarin har sai wannan satin,a lokacin da jama a suka yanke shawarar shiga gidan domin cire ganyayyaki da ciyawun da sukayi yawa har sun fara haddasa majizai a layin.

An tara mutanen da akayi ciniki dasu zasuyi aikin cire ciyawun,inda suka haura ta katanga tunda gate din gidan kulle yake.

Bayan sun haurane sukaga Ashe motar maigidan tana nan har ganyayyaki da ciyawu sun lullubeta.

A cewar wadanda suka gani da ido, Kamar Yadda ALFIJIR HAUSA ke Samun tabbacin lamarin; bayan anyi kokarin cire ganyayyakin ne aka leka ta taga inda sukaga kwarangwal din mutum kwance bisa gado rike da waya a hannunsa.

Jami’an yan sanda na garin oyo suna cigaba da bencike akan lamarin.

Ku kasance masu duba yan uwanku.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN