Labari Da Dumi Duminsa ~ Gwamnatin kano ta fara zartar da hukuncin da kotu ta yi kan Abduljabbar
Labari Da Dumi Duminsa ~ Gwamnatin kano ta fara zartar da hukuncin da kotu ta yi kan Abduljabbar
Gwamnatin jihar Kano ta fara zartar da hukunce-hukuncen Alkalin Babbar Kotun Shari’ar musulunci ta yanke wa Malamin na Kano, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wanda aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin aikata batanci ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
Dadai Bidiyon
Majiyar mu ta rawaito cewa Alkalin Kotun, Malam Ibrahim Sarki Yola yayin da yake yanke hukuncin a ranar 15 ga Disamba, 2022 ya ce hukuncin da ya biyo baya ya zama dole don hana ci gaba da yi ko yada kalaman batanci ga Fiyayyen halitta S A W.
Justice Watch News ta tattaro cewa mataimakin Sheriff na babbar kotun jihar Kano ya zartar da hukuncin a jiya juma’a.
Yayin da wakilinmu ya ziyarci masallacin Ashabul Kahfi da ke Filin Mushe a karamar hukumar Gwale da Masallacin Jamiurrasul da ke Sabuwar Gandu a cikin birnin Kano a ranar Asabar din nan, ya lura da cewa masallatan biyu da makarantar na wanda aka yankewa hukuncin, an kulle su Kuma suna karkashin kulawar jami’an tsaro da ke dauke da manyan makamai.
Hakazalika jaridar Justice Watch ta tattaro cewa dukkan littafai 189 da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayar a lokacin shari’ar an kwace su tare da kai su zuwa dakin karatu na jihar Kano kamar yadda kotu ta bayar da umarni.
Gadai Bidiyon
A kwanan baya ne dai kotu ta zartarwa da malamin hukuncin kisa, tare da bada umarnin kwace littattafan sa da rufe masallacin sa wanda yanzu aka fara aiwatar wa.
Masana Shari’a sun bayyana cewa Gwamnati zata aiwatar da fille kan Malam Abduljabbar ne idan ya gaza daukaka ƙara nan da kwanaki 30