Labaran duniya
Tofa! Mafarauci Ya Harbe Wani Mutum Har lahira bisa tunanin cewa Wai ya zaci Tsuntsu ne a jahar Kano
Subhanallahi Gadai Bidiyon a kasa
Da sanyin safiyar yau ne, kafar yada labarai ta BBC Pidgin ta rawaito cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wani mafarauci mai suna Muhammadu Basiru dan shekara talatin da biyu (32) bisa zargin kashe wani a lokacin da yake kokarin harbin wani tsuntsu a daji.
Da yake bayyana mummunan lamarin,
maharbin yace, “Ban gudu ba bayan harbe
shi ba. Na dauka tsuntsu ne a cikin daji.
Mafarauci ya ba da labarin yadda ya kwashe sama da shekaru shida yana farauta da bindigar ahi. Ya kara da cewa, “A ranar da na mayar da hankali na shi ne in harbe tsuntsun saboda ban lura cewa wani yana kusa da tsuntsun ba.”