Labaran duniya

Malamai Sun Fusata Cikin fushi da bacin rai sunyi kira ga Gwamnati akan Kashe Malam da Sojoji sukayi

Muna Kira Ga Gwamnatin Tarayya Da Ta Gaggauta Hukunta Sojojin Da Suka Kashe Sheikh Goni Aisami, Cewar Kungiyar Izala

Shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukan mataki Akan wasu sojojin Naijeriya guda biyu da suka kashe daya daga cikin malaman kungiyar Sheikh Gwani Aisami dake garin Gashua ta jihar yobe.

Shehin Malamin ya Kara da cewa “Muna yabawa hukumar ‘yan sanda da suka dauki mataki nan take na cafke sojojin da a ka samu a daji wajen gawar marigayin.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a Yobe Dungus Abdulkarim ya tabbatar da kama sojojin kuma ya ce bayan kammala bincike zai yi karin bayani kan akasin.

Rahotanni da su ka karade yanar gizo sun nuna Shehun Malamin na dawowa Gashua ne daga tafiyar da ya yi zuwa Kano sai wani soja ya bukaci ya rage ma sa hanya zuwa garin Jajimaji a yankin Karasuwa. A lokacin Sheikh Aisami ya tsaya kama ruwa ashe sojan na son sace ma sa mota ne don haka da ya dawo sai ya yi ma sa barazana da bindiga a kan ya iso wajen motar.

Marigayi Sheikh Goni Aisami ya dage don zuwa wajen dukiyar sa inda sojan ya bude ma sa wuta ya kashe shi.
Yayin da ya yi ta kokarin tada motar ta ki tashi sai ya kira wani abokin aikin sa wanda ya zo da motar sa amma ita ma ta samu matsala don haka duk su ka samu taimako daga ‘yan sintiri.

A sanadiyyar zuwan ‘yan sintiri ne su ka fahimci akwai matsala inda su ka ankarar da ‘yan sanda su ka zo su ka cafke sojojin biyu.

Sheikh Bala Lau yace babu shakka kungiyar baza ta amince Akan wannan ta’addanci ba, yace sun zura ido da kunnuwa domin sauraren yadda zata kaya wajen aiwatar musu da hukunci cikin gaggawa.

Sheikh Lau Ya kuma mika ta’aziyyar kungiyar ga ‘yan uwa da iyalai da al’ummar garin Gashua da jihar yobe, dama kasa Baki daya na rashin Sheikh Gwani Aisami, da fatan Allah ya karbi shadarsa,ya kyautata makwancinsa, ya hadamu a aljanna firdausi Baki dayan mu. Amin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN