Masha Allah ~ Aljannu Bilyan 3 Ne Suka Karɓi Ɗaríkar Tíjjaniyya A Bana – Cewar Sheíkh Ɗahiru Bauchi
Aljannu Bilyan 3 Ne Suka Karɓi Ɗaríkar Tíjjaniyya A Bana – Cewar Sheíkh Ɗahiru Bauchi
Babban Malamín Ɗariƙar Tijjaníya wato Sheíkh Ɗahíru Usman Bauchí ya ce Aljannu Biliyan Uku sun karɓi Ɗarikar Tijjaniya.”
“Babban Malamin ya ƙara da cewa, daga cikin wadannan Aljanu, akwai Mukaddamai miliyan dari biyu Cif-Cif.”
Gadai Bidiyon:
▶️ PLAY
Cikekken bayanin tare da Bidiyon suna can Kasa.
Sheikh Dahiru Bauchi Ya Cika Shekaru 98 A Duniya A Lissafin Hijriyya (1,346-1,444)
Shahararren Malamin addinin Islama a fadin duniya kuma mataimakin shugaban masu fatawa na Nijeriya kuma babban Shehin Darikar Tijjaniyya a duniya Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA ya cika shekaru 98 a duniya a lissafin hijriyya (1,346-1444).
PLAY ▶️
Sheikh Dahiru Bauchi an haife shi a karamar hukumar Nafada dake jihar Gombe, ya taso a gaban mahaifansa inda ya fara karatun Alkur’ani mai girma a gaban su, daga baya ya shiga neman karatun inda har Allah ya azurta shi da samun Alkur’ani mai girma tare da sauran littafan addinin Musulunci har ya zama masu shahara a wannan zamani.
Sheikh Dahiru Bauchi RA, ya zama babban malamin a fadin duniya, wanda a yanzu shine mataimakin shugaban masu fatwa na Addini Musulunci a najeriya, kuma khalifan Sheikh Ibrahim Inyass ne a duniya baki daya.
PLAY ▶️
Shehin Nalamin yana da ya’ya maza da mata, wadanda mafi yawan su mahaddata Alkur’ani ne tare da dimbin jikokin sama da dari biyu 200, a yanzu yana zaune a garin Bauchi dake arewacin Najeriya.
Allah ya albarkacin rayuwar sa ya kara lafiya da daukaka ya kara masa himma wurin hidimtawa addini Musulunci da darikar Tijjaniyya a fadin duniya. Amiin Yaa ALLAH.
Daga Babangida A. Maina
Tijjaniyya Media News