Labaran duniya

Masha Allah! Ashe Sarauniyar England ‘Queen Elizabeth’ ta Musulunta kafun Rasuwar ta

Ko Sarauniyar England ta karbi Musulunci kafin mutuwar ta?

Labarin mutuwar Queen Elizabeth ya tabbata, bayan ‘kararrawar fadar Masarautar Burtaniya ta kada a karo na biyu cikin shekaru 70.

Queen Elizabeth ta biyu (ll) ta gaji sarautar Britannia ne bayan Mahaifin ta King George VI ya rasu a shekarar 1952, a shekarar aka nada ta a ranar 06 February 1952 (shekaru 70 da suka wuce), an rantsar da ita a matsayin Sarauniyar England da Commons wealth a 1 June 1952 din.

Queen Elizabeth ll an haife ta a yankin “Mayfair” dake London a shekarar 1926 (shekaru 96 da suka wuce).
Tayi Sarauta na tsawon shekaru 70 da kwanaki 214.

Queen Elizabeth itace Mai Sarautar Gargajiya mafi dadewa a tarihin Masarautar Burtaniya, Sarauniyar Elizabeth itace shugaban kasa a England (Head of State), yayn da duk wanda aka zaba Prime Minister shi yake zama shugaban gwamnati.
Turawan England suna matukan girmama Queen da riko da dukkan tsarin ta.

Elizabeth ta auri Yarima Philip Duke a 1947, auren su ya dade na tsawon shekaru 70, Prince Philip Duke ya mutu a 2021.
Suna da ‘ya’ya 4 da Queen Elizabeth.

Sai dai wata magana da ake cewa an boye ta game da Queen Elizabeth shine batun Musuluncin ta ko rashin sa.
Akwai maganganu masu karfi daga cikin gidan Sarautar cewa a shekarar 2012 Queen tayi yunkurin Musulunta amma aka hana ta, daga bisani ta sake yunkurin hakan a 2015 shima dai bai yiwu ba.

Abinda ake cewa shine ana kyautata zaton ta Musulunta a boye, saboda yadda aka ga ta sassauta tsare tsaren gwamnatin ta, da kuma alakar ta da Musulmi da kasashen su.

A baya bayan nan tayi ta ziyarar manyan masallatai a duniya, ance taso zuwa Ka’abah amma an tabbatar mata ba zai yiwu ba a matsayin da take.
Daga karshe karshen rayuwar ta anyi ta ganin ta sanye da Kallabi (‘Dankwali) da tufafin dake nuna Sarauniyar ta sauya.

Sai dai koda Elizabeth ta Musulunta, Musuluncin bai bayyana ba, amma rahotanni da dama suna ishara da tabbatuwar Musuluncin nata.

Muna fata Allah yasa ta kasance daga cikin sahun Sarki Jajjashi.
Amma gaskiya mu dai a wajen mu Musuluncin ta na hakika bai bayyana mana ba, watakil wasu sun fi gamsuwa da cewa ta Musulunta shiyasa suke mata addu’o’in neman Rahama.

A irin wannan yanayin, mun tsaya a matsayin yin shiru game da ita, saboda mun samu shakka game da ita, bamu da tabbacin Musuluncin ta bare muyi mata addu’o’in neman Rahama.

Allah ya baiwa kasar England Sarkin da zai zame musu mafi alkhairi.

Abdul-Hadi Isah Ibrahim.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN