Biography

Masha Allah Kalli Bidiyon Yaddá Ƙayataccén Gídan Zinari Ná Márigayi Attajiri Alhaji Mai Déribe Yaké Á Birnin Maiduguri Gidan da babu mai sadanta a kaf Africa

Ƙayataccen Gidan Zinari Na Marigayi Attajiri Mai Deribe A Maiduguri, Mutumin Da Ya Fi Kowa Kudi A Nijeriya A Shekarun Baya

Marigayi Alhaji Mai Deribe yana ɗaya daga cikin hamshaƙan masu kuɗin Afrika da suka mori dukiyarsu kuma har duniya ta dinga sha’awarsu.

GADAI BIDIYON CIKIN GIDAN KAI TSAYE:

Deribe ya gina wata gagagrumar fada a Maiduguri wacce magina suka kwashe shekaru 10 suna aikinita kafin su kammala.

Daga cikin manyan mutane a duniya da fadar ta bai wa masauki akwai tsohon shugaban ƙasar Amurka, Geroge Bush da Olusegun Obasanjo, Marigayi Alhaji Mai Deribe babu shakka yana ɗaya daga cikin hamshakan masu kuɗi a Nijeriya a shekarun 1980.

GADAI BIDIYON CIKIN GIDAN KAI TSAYE:

Mai Deribe yana cikin attajirai guda 12 a duniya da suka mallaki wani jirgin sama mai ƙirar Gulfstream G550 a shekarar 1971.

Ya gina gida wanda aka yi shi da ruwan zinari.

Gidan, wanda ake kira da Gidan Deribe, ya ja hankulan jama’a masu tarin yawa a duniya. Ba abun mamaki bane ganin yadda ya dinga saukar manyan mutane a duniya kamar Yarima Charles da matarsa, marigayiya Gimbiya Diana.

Wadanda suka taba shiga Gidan Deribe akwai tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Sarki Juan Carlos na ƙasar Spain da tsohon shugaban kasar Amurka, George Bush, Shugaban kasar mulkin soja na wancan lokacin, Janar Ibrahim Babangida, shi ya jagoranci buɗe fadar zinarin bayan kammala ginin da aka yi.

GADAI HOTUNAN CIKIN GIDAN KAI TSAYE:

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
KALLI BIDIYON ANAN