Masha’Allah Biki yayi Biki ~ Kalli Bidiyo Kai Tsaye daga Wajan Daurin Auren ABALE
Abale ya Shiga daga Ciki ayau Juma’a.
Fitaccen Jarumin na Kannywood Adam Abdullahi Adam wanda aka fi sani da Daddy Hikima (Abale) ya shiga daga ciki ne ayau ranar juma’a 27-01-2023.
Inda aka ɗaura Auren, a masallacin Uhud dake Unguwar Naibawa a ƙaramar hukumar Kumbotso jihar Kano, tare da amaryar sa mai suna, Maryam Farouk Sale.
Mutane da dama sun Halarci daurin Ciki Harda Manyan yan Siyasa da Manyan Jaruman kannywood wanda a yanzu haka zamu saka muku Bidiyon ku kalla.
Gadai Bidiyon Kai Tsaye
Yawan fitowarsa a matsayin dan daba ya sa hatta wasu wadanda suka san shi a baya mantawa cewa dan boko ne.
Daddy Hikima wanda haifaffen Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano ne, ya yi karatun boko har zuwa matakin zama nas a Kwalejin Kiwon Lafiya (ta Hygiene) da ke Kano bayan ya yi sakandare a Dawakin Tofa.
Daddy Hikima ya dade a yana aiki a masana’antar Kannywood a matsayin mai shirya wajen daukar shiri (Production Manager), ko kuma aikin cigaban shiri da yayi fice a kai, wato Continuity.
Bayan zuwan sinima, sai Daddy ya zama daya daga cikin masu sayar da tikitin shiga kallon fim a sinima da ke Ado Bayero Mall Kano.
Yawanci ba a cika damuwa da shi ba idan ana haska fim, saboda yawancin ana zuwa ne domin ganin manyan jarumai da ke zuwa kallon fim.