Labaran Kannywood
Matar marigayi jarumin shirin Kwana Casa’in Umar Malunfashi ta bayyana yadda suka yi bankwana da shi
A cewar matar marigayi Umar Malunfashi tace: tun da aka yi masa allurar dauke radadi yayi bacci sakamakon zafin aikin mafitsara, bai sake farkawa ba da haka Allah ya karbi rayuwar sa.
Malam Umar Malumfashi ya shafe tsawon watanni yana jinya a asibiti inda matarsa tana gayawa manema labarai sunyi jinya a asibiti yakai sau uku.
Muna yiwa malam Umar Malunfashi addu’ar Allah ya jikansa yayi masa rahama da dukkan musulmai wadanda suka rigamu gidan gaskiya.
Domin kuji cikekkiyar shirar da aka yi da matar marigayin sai ku kalli bidiyon dake kasa
Gadai Bidiyon: