Matashi Ya Kashe Iyayensa da tabarya wai ya Fahimci Basa kaunar Annabi SAW
Matashin da ya kashe iyayensa da taɓarya mahaukaci ne tuburan – Inji yan uwansa
Matashin dai ya shara wa jami’an tsaro karyar cewa iyayen nasa ba sa kaunar wakar da yake wa Manzon Allah SAW shi ya sa ya kashe su da tabarya
Bayanai da ke fitowa daga kauyen Zarada Sabuwa na karamar hukumar Gagarawa ta jihar Jigawa a arewa maso yammacin Najeriya, na nuni da cewa wani mutun da ya kashe mahaifi da mahaifiyarsa, na fama da tabin hakanli.
Mutumin mai suna Munkaila Ahamadu, dan kimanin shekaru 37, ya dokawa mahaifan nasa tabarya a kwanyar kai, al’amarin da yayi sanadiyyar mutuwar su nan take.
Dangin mutumin sun fada wa muryar Amurka cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis bayan sallar azahar, lokacin da Munkaila ya shiga gidansu, inda yayi yunkurin saduwa da matar kaninsa da karfin tuwo, sai ta yi masa kuwwa tana neman agaji daga mutanen gida.
Ihun da ta kwarmata ne ya jawo hankalin mutane, ciki har da mahaifinsa wanda bai dade da dawowa daga gona ba a lokacin. Cikin fushi da bacin rai mahaifin nasa yayi masa fada tare da nasiha game da abin kunyar da ya yi. Hakan ya fusata Munkaila Ahmadu kuma nan take ya dauko tabarya a tsakar gida ya bugawa mahaifin nasa a kwanyar kai, abinda ya sa ya sume nan take.
Ana tsaka da haka, sai mahaifiyar Munkaila ta shigo gidan ta ga abinda ya faru. Cikin firgici da tashin hankali ta kama Munkaila da fada har tayi kokarin kwace tabaryar da ke hannunsa, al’amarin da ya kara fusata shi ya yi kokarin kai mata duka sai ta kauce, amma duk da haka ya bita ya kwantsama mata wannan tabarya, abinda yayi sanadiyyar mutuwar ta gabanin a je asibiti.
Sai dai wani mai suna Malam Salihu Zarada, da ke zaman suruki ga mahaifiyar Munkaila Ahmadu, ya shaida wa Muryar Amurka cewa, shi Munkaila da yayi wannan kisan ya jima yana fama da tabin hankali, kuma abin ya motsa tun a makon jiya, inda ya fara surutai barkatai.
A cewar Malam Salihu Zarada Sabuwa, Munkaila wanda ya taba yin takarar kansila a kauyensu, ana zargin ya gamu da lalurar kwakwalwa ne sakamakon sana’ar korar aljanu a jikin mutane da yayi a baya. Ya ce tun wancan lokacin dabi’un sa suka canza kuma kwakwalwar ta zama bata da saiti.
Duk da cewa an yi kokarin yi masa magani, ba’a taba kai shi gidan kula da masu tabin hankali na gwamnati ba.
Tuni dai rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mahaifan Munkaila, kuma ta shaida cewa jami’anta sun kama shi.
Malam Salihu Zarada Sabuwa ya kuma fadi cewa an yi jana’izar mamatan tun ranar da lamarin ya faru, kuma jami’ai sun wuce da Munkaila zuwa cibiyar kula da masu tabin hankali ta gwamnatin Jigawa da ke garin Kazaure.
A hannu guda kuma wani makwabcinsu Munkaila da ya kawo dauki lokacin da ya ji hayaniya ta kaure a gidan bisa tsammanin katanga ko daki ne ya fadi, yana kwance a asibiti sakamakon raunin da ya samu a hatsaniyar.