Menene Hukuncin fitar da maniyya da Gangan a azumi ~ Malam Aminu Daurawa
Menene Hukuncin fitar da maniyya da Gangan a azumi ~ Malam Aminu Daurawa
Wani Bawan Allah ya aiko wa Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa tambaya, inda ya nemi fatawa a kan zubar da maniyyi a lokacin da mutum yake azumi.
Wannan mutum ya bayyana cewa ya na cikin yin waya da budurwarsa a wayar salula, sai ya ji maniyyi ya fito daga gabansa, alhali azumi ya na bakinsa. Kafin ya amsa tambayar, babban malamin na musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ja-kunne a kan yin waya irin wannan a lokacin da ake azumi.
GADAI BIDIYON
Aminu Ibrahim Daurawa ya nakalto fatawar babban malamin fikihu nan, Ibn Abi Zayd Al-Qayrawani, wanda ya ce irin azumin wannan Bawan Allah ya karye. Sheikh Al-Qayrawani a littafinsa na Risala, ya ce wanda ya zubar da maziyyi da gangan a sanadiyyar sha’awa zai kama baki, sai ya rama azumi daya daga baya.
Haka zalika a fatawar bajimin malamin, duk wanda ya kai har ga zubar da maniyyi a lokacin azumi, sai ya yi kaffara; zai yi azumi 61 bayan watan na Ramadan.