Kannywood

Muja Kunya Tayi Kira Ga Hukumar Hisbah da tayi musu gwajin Kanjamau tare da Matan Kannywood

TIRƘASHI: Muja Kunya Tayi Kira Ga Shugaban Hukumar Hisbah Sheikh Daurawa Da Ya Tattaro Dukkan Matan Kannywood Harda Ita Aje Ayi Musu Gwajin Cutar Kanjamau A Nuna Kai Tsaye Live

Dangane da dambarwar da ke faruwa kan masana’antar Kannywood, Murja Kunya ta maida martani, ta kuma yi kira ga shugaban hukumar HISBAH ya tattaro su gabaɗaya a yi musu gwajin HIV, kamar yadda Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito cikin wani bidiyo da Murja ɗin ta saki a shafinta.

A cewar shahararriyar jarumar Tik-Tok Murja Ibrahim Kunya ita da kanta ta san yarinyar da ta rasa ranta sanadiyyar lalata mata dubura da aka yi har a gadon asibiti aka kwantar da ita tsuttsotsi ne su ke fitowa daga bayanta.

Murja ta cigaba da cewa sai da ta kai ta kawo gunduwa-gunduwar nama ake sayowa a cusa a cikin duburar Yarinyar tsutsotsin su riƙa cin naman a madadin su ci naman jikinta wanda wannan matsala kuma ita ce ta yi snadiyyar mutuwarta.

Murja ta ƙara da akwai mata da dama waɗanda an daina yayinsu sun koma kawalci sai dai su kai ƴan mata ƙanana, saboda su an gaji da su.

Hatta aikin Haji da ƴan mata da dama su ke zuwa a cewar Murja Kunya ba ibada ce ta ke kai su ba, nemansu ake yi a biya musu kuɗin jirgi su je.

Murja ta yi kira ga shugaban hukumar HISBAH ta haɗa shi da Allah ya nemo likita mai tsoron Allah a haɗa mata Jarumai na Kannywood gabaɗaya har da su Murja ɗin a kuma haska Bidiyo Live a yi musu gwajin cutar ƙanjamau wato HIV/AIDS.

Shin ku na ganin ya kamata a gayyaci jarumai mata na masana’antar Kannywood a yi musu gwajin HIV ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN