Labaran duniya

Mutum Zai Iya Zama Ɗan Shi’ah, Kuma Ya Na Tijjaniyyah~Inji Shaikh Zakzaky

Mutum Zai Iya Zama Ɗan Shi’ah, Kuma Ya Na Tijjaniyyah-Inji Shaikh Zakzaky

Daga Mujaheed Umar D Giwa

Shaikh Ibraheem Zakzaky yayi gyara wa wayenda suke ganin cewa dole sai sun bar ɗariƙa ne kafin su zama Shi’ah,

Inda Shaikh ɗin ya ke cewa: Ba dole ne sai mutum ya bar Darika ba sannan ya zama Shi’a, ana iya hada duk biyun in an so, saboda daya Mazhaba ce, dayan kuma matafiyar Irfani ko Tasawwuf ce, ba bukatar sai mutum ya bar Tijjaniyya (kafin ya zama Shi’a). Mazhabar Malikiyya ne mutum zai bari sannan ya zama (mai bin Mazahabar) Jafariyya (Shi’a), amma yana iya yin Tijjaniyya.”

Shaikh Zakzaky ya kara da cewa: “Idan mutum Shi’a ne, zai iya yin Qadiriyya zai iya yin Tijjaniyya, kuma yana Shi’arsa. Amma Mazhaba akwai ta Jafariyya (ba zai yi Malikiyya ba).

Yace “Akwai bangarorin karatu a addinin nan guda uku muhimmai; na daya muna ce masa Tauhidi, wanda yake magana kan abubuwan da ya zama dole mutum ya yi imani da su, duk abin da za ka yi I’itikadinsa a zuciya shi yake magana a kai. Wato yana magana dangane da Allah, da Manzo da Annabta da ranar Lahira, duk abin da zai zama dole ka yi I’itikadinsu ka yarda da su, shi Tauhidi ke magana a kai. Wannan kamar yadda ake da Mazhaba a bangaren Fikihu, ana da abin da ake kira Firqa a bangaren Tauhidi, ko a bangaren Ahlussunnah akwai Ash’ariyya akwai Maturidiyya da sauransu, duk suna magana kan Aqa’id ne.

Shehin Malamin yace”Abu na biyu shi ne Mazhaba, wanda shi kuma yana magana dangane da Hukunce-hukunce ne, yadda za a yi ibada da mu’amaloli. Ibadodi sun hada da irin su sallah, azumi, zakka, hajji. Mu’amaloli kuma akwai aure, rabon gado, ciniki da ire-irensu. Mene ne wajibi, mene ne haramun, mene ne mustahabi, mene ne makaruhi, to shine abin da Fiqihu yake koyarwa. To a wannan ne ake samun Mazhabobi. Shine aka samu a tsakanin Ahlussunnah akwai Malikiyya, Shafi’iyya, Hanafiyya da Hambaliyya, wadannan ne fitattun mazhabobi guda hudu, amma akwai wasu (kari), wadannan kawai sun shahara ne. Haka nan kuma aka samu (Mazhabar) Jafariyya a bangaren Shi’a.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN