Labaran duniya

Na Bada Cin Hanci Domin Fita Daga Kurkuku Amma Abu Ya Gagara – Sheikh Abduljabbar Kabara

Kano: Na Bada Cin Hanci Domin Fita Daga Kurkuku Amma Abu Ya Gagara – Sheikh Abduljabbar Kabara

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara wanda ake zargi da laifin batanci ya zargi Lauyansa, Dalhatu Shehu-Usman da laifin karbar cin hancin kudi daga hannunsa.

Kamfanin dillacin labarai na kasa yace Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara yana tuhumar Dalhatu Shehu-Usman da karbar N2m domin ya ba Alkali rashawa. Shehin malamin da ake kara, ya bukaci kotu tayi watsi da ƙarar da aka shigar a kan shi, a kuma sallame shi, sannan a umarci gwamnatin jihar Kano ta nemi afuwarsa.

“Ina rokon kotu ta karbi korafin da muka rubuta a wannan shaida a matsayin hujja a kan zargin wa’adin da nayi. Lauyana ya same ni a kurkuku Lauyana ya zo gidan yari, ya fada mani cewa Alkali ya umarce shi ya biya Naira miliyan 2 da nufin a wanke ni.

Lauyan nawa ya fadi mani ya ba Alkali N1.3m, sai ya ba wani mutum N200,000, shi karon kansa ya dauki N500, 000.”

An gama sauraron kara Lauyan masu kara, Mamman Lawan-Yusufari SAN ya gama shigar da karansa yayin da ya kira mutane hudu su bada shaida a zaman kotun da aka yi, shi kuwa Malamin da ake kara ya kawo mutum daya a matsayin shaida, sannan ya kafa hujjoji da littatafai 24 da kuma faifen karatun da ya gabatar a baya.

Mai shari’a Ibrahim Sarki-Yola ya yi watsi da zargin da ake yi masa, yace bai karbi cin hanci daga hannun Lauyan malamin ko wani ba. Ibrahim Sarki-Yola yace zai bada sanarwar ranar da kotu za ta sake yin zama domin sauraron karar.

Shi ma Lauyan da yake kare Sheikh Kabara, Shehu-Usman ya shaidawa manema labarai cewa bai yi mamakin jin malamin ya jefe shi da wannan zargi ba. Lauyan yana cewa dama can sai da wanda ake tuhuma ya samu matsala da lauyoyi uku da suka yunkurin kare shi.

“Wannan magana karya ce; Ni ban yi mamaki ba domin wannan halinsa ne. “Idan an duba, ya yi makamancin irin wannan zargi a kan lauyoyinsa kafin ni. a cikinsu ma akwai wadanda ya zarga da neman matarsa.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN