Labaran Kannywood

Na Ranse da Allah babu abunda zai Hanani Cin zabe inba Mutuwa ba a 2023 – Bola Ahmad Tinubu

KARON BATTAR 2023: Tinubu garau ya ke, kwana ya ke aiki wurjanjan, Peter Obi tantirin maƙaryaci ne –

-Kakakin Kamfen ɗin Asiwaju 2023

Kakakin Yaɗa Labaran takarar shugaban ƙasa ta Bola Tinubu a APC, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa Peter Obi tantirin maƙaryaci ne da ya ce Tinubu ba shi da ƙwarin jikin da zai iya shugabancin Najeriya.

Onanuga ya maida masa wannan raddi ne bayan Obi wanda ke takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin LP ya yi iƙirarin cewa Tinubu ba shi da ƙoshin lafiyar da zai takarar shugaban ƙasa, ballanata shugabancin ƙasa.

Ya ce Tinubu garau ya ke, kuma a kullum ya na aiki sa’o’i 20 ya na kuma ganawa da mutane ana tattauna batutuwan yadda za a bunƙasa Najeriya.

“Banda ƙarairayi da shirme ai Peter Obi bai iya komai ba? Ta yaya kai da ba likitan mutum ba za ka iya iƙirarin cewa ba shi da lafiya.

Obi dai ya ce ko waɗanda ke kewaye da Tinubu sun san cewa ba shi da lafiya, “amma su na bin sane don kawai su samu kuɗi a jikin sa.”

Shi kuma Onanuga cewa ya yi kowa ya san Tinubu ne ya fi cancantar ceto Najeriya, saboda ya yi an gani a jihar Legas. “Shi kuma Peter Obi da ya yi gwamna bai tsinana komai ba sai burga da ƙarairayi kawai.

Peter Obi tun da farko ya zargi makusantan Tinubu cewa sun riƙa watsa bayanai a soshiyal midiya su na cewa kada a zaɓi Obi, domin idan aka zaɓe shi, “ƙabilar Igbo za su daina zuwa Legas, komawa za su yi gida su raya yankin Kudu maso Gabas.

Dama kuma kwana biyu da su ka gabata, Femi Fani-Kayode da Festus Keyamo sun maida wa Peter Obi raddin cewa Tinubu ba zai janye daga takarar 2023 ba.

Majalisar Kamfen ɗin Tinubu 2023 ta yi tofin Allah-wadai kan wani rahoto da ke yawo a soshiyal midiya mai nuna cewa wai Bola Tinubu zai janye daga takarar 2023, saboda rashin lafiyar da ke damun sa.

Cikin wata sanarwar da Femi Fani-Kayode, ɗaya daga cikin Kakakin Yaɗa Labaran Kamfen ɗin TInubu 2023 ya fitar a ranar Litinin, ya ce rahoton labari ne na ƙarya, bogi ne, jabu ne wanda magoya bayan Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP s

Kuma mai girma Bola ahmad Tinubu Ya bayyana mana cewa in Allah ya yarda mine zamuci zaben bana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN