Labaran duniya

Na rantse da Allah Mauludi bidi’a ne, mun faɗawa gwamnatin ƙasar nan amma har yanzu taki daukan mataki, tare da hana hutun Mauludi.

Na rantse da Allah Mauludi bidi’a ne, mun faɗawa gwamnatin ƙasar nan amma har yanzu taki daukan mataki, tare da hana hutun Mauludi.

To kowa ya sani cewa, indai wadan da suke jin maganar mu su kafa gwamnati sai munsa an soke hutun maulidi a Nigeria, Cewar ~ Sheikh Gumi

Ba’a San yin bikin maulidi a Makka da Madina lokacin manzon Allah- “Inji Dr. Ahmad Gumi.

“Shin wace riba ka samu? Me ya chanja a rayurka da al-amarin Musulmai?

Allah – subhanahu Wa ta’ala- Yana cewa:

ﵟوَلَا ‌تَقۡفُ مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٌۚ إِنَّ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡبَصَرَ وَٱلۡفُؤَادَ كُلُّ أُوْلَٰٓئِكَ كَانَ عَنۡهُ مَسۡـُٔولٗا ﵞ [الإسراء: 36]
Ma’ana:
“Kuma kada ka bi abin da bã ka da ilmi game da shi. Lalle ne jĩ da gani da zũciya, dukan waɗancan (mutum) yã kasance daga gare shi wanda ake tambaya.”

Kuma a cikin Wani Hadisi

>أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «‌مَنْ ‌عَمِلَ ‌عَمَلًا لَيْسَ عَلَيْهِ أَمْرُنَا فَهُوَ رَدٌّ< متفق عليه
Manzon Allah Tsira Da aminicin Allahcsu tabbata a gareshi- yace: “ duk wanda yayi wani aikin da babu umurnin mu a kansa toh aikin an maida mishi”

Kuma a cikin Al-ahalari:

«وَلَا يَحِلُّ لَهُ أَنْ يَفْعَلَ فِعْلًا حَتَّى يَعْلَمَ ‌حُكْمَ ‌اللَّهِ فِيهِ وَيَسْأَلَ الْعُلَمَاءَ وَيَقْتَدِيَ بِالْمُتَّبِعِينَ لِسُنَّةِ مُحَمَّدٍ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ اَلَّذِينَ يَدُلُّونَ عَلَى طَاعَةِ اللَّهِ، وَيُحَذِّرُونَ مِنَ اتِّبَاعِ الشَّيْطَانِ» «متن الأخضري في العبادات على مذهب الإمام مالك» (ص4):
“kuma baya halatta gareshi da ya aikata wani aiki har sai san hukuncin Allah a cikin shi, kuma ya tambayi malamai kuma yayi koyi da malaman da suke bin sunnar Muhammadu tsira da aminicin Allah su tabbata a gareshi- waɗanda suke nuni zuwa ga yiwa Allah ɗa’a kuma suke gargaɗi akan bin shaiɗani.

Ka sani fa, babu babin Maulidi acikin litattafan fikihu na ibada kamar Qawaidi, da ahalari, da askari, da ashmawi, da izziyya, da risala, da mukhtasar domin yin Maulidi Bidia ne a wurin malikiyah gaba daya. Ba’a san yin bukin maulidi a madina da makkah alokacin Manzon Allah Tsira Da aminicin Allahsu tabbata a gareshi- da sahabbai da tabi ai da tabiut’ tabi iani.

Saboda haka, me ka mora yin abinda ba ibada ba ko addini?

Na daya, kayi abinda ke dawwammar da rabuwar al-ummar muhmmad domin kamar yadda Hadisi ya zo ba kowa zai yadda da bidi’a ba:
عَنِ ‌الْمُغِيرَةِ بْنِ شُعْبَةَ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ قَالَ: «لَا يَزَالُ ‌طَائِفَةٌ ‌مِنْ ‌أُمَّتِي ظَاهِرِينَ، حَتَّى يَأْتِيَهُمْ أَمْرُ اللهِ وَهُمْ ظَاهِرُونَ.» متفق عليه
“Ma’ana: Wata kungiya daga al-ummata ba zata gushe ba tana cin nasara har sai al-amarin Allah ya zo masu alhali suna masu cin nasara”

“Na biyu, kayi koyi da Nasara. Na uku, kayi girmamawar da sharia ba tazo da shi ba a haƙƙin manzon Allah (S.A.W.) Na huɗu, ka taimaka

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN