Labaran Kannywood

Ko Kaɗan Finafinan Hausa Basa Ɓata Tarbiyya Sai Dai In Dama Can Yaranku Basu Da Tarbiyya A Gida, Nafisa Abdullahi

Ko Kaɗan Finafinan Hausa Basa Ɓata Tarbiyya Sai Dai In Dama Can Yaranku Basu Da Tarbiyya A Gida, Nafisa Abdullahi Ta Caccaki Masu Sukar Finafinan Hausa
Shahararriyar jarumar nan ta masana’antar finafinan Kannywood, Nafisa Abdullahi tayi kalamai masu kaushi akan mutanen dake sukar finafinan Hausa.

Nafisa Abdullahi a wani rubutu da tayi a shafin ta na Twitter tace ko kaɗan finafinan Hausa ba sa ɓata tarbiyyar yara sai dai idan dama can asali yaran ba su samu tarbiyya a gida ba.

“Ba yadda za a yi mutane su bar yaran su na kallon finanfinan ƙasar Amurka (Hollywood), finafinan Indiya (Bollywood) dana kudancin Najeriya (Nollywood), sannan su buɗe baki suce finafinan Hausa ne ke ɓata tarbiyyarsu.” Inji ta

Mutane da dama dai na ganin cewa finafinan Hausa na wannan zamanin na zama wani abin gurɓata tarbiyyar yara, musamman yadda ake nuna wasu abubuwan da suka ci karo da al’adar Hausawa.

An sha korafi akan yadda masana’antar ta koma nuna wasu abubuwa waɗanda suka ci karo da ɗabi’a da al’adar Hausawa, sai dai jarumar na ganin cewa masana’antar bata ɓata tarbiyya.

Source: Idon Makiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN