Labaran duniya

Nayi Damar Karuwanci Da Irin Barikin Da Nai A Baya ~ A Cewar Muneerat Abdulsalam Bayan Tasha Dukan Tsiya A Wurin Saurayinta

Nayi Damar Karuwanci Da Irin Barikin Da Nai A Baya ~ A Cewar Muneerat Abdulsalam Bayan Tasha Dukan Tsiya A Wurin Saurayinta

Daga Salisu Magaji Fandalla’fih

Sananniyar Mai amfani da kafafen sadarwa tana furta kalaman batsa, da baɗala Muneerat Abdulsalam tace tayi Nadamar abubuwan da ta aikata a rayuwar ta.

Jarumar ta bayyana cewa tayi wani saurayin da suke ƙoƙarin yin Aure amma kuma daga baya ta fahimci cewa bayada halaye masu kyau a dan haka ta gudu ta rabu dashi, daga baya ya ganota yakuma lakaɗama ta duka.

Ga saƙon ta da ta rubuta a Shafin ta na Facebook👇

“Oh ni Muneerat Abdulsalam haka rayuwata ta koma? Ko kudin sayan paracetamol banidashi kuma ba mai bani, na zama abin kwatance a idon duniya, gani ga wane ya ishi wanne soron Allah, nayi nadaman duka karuwancinda nayi diga baya, da duka shashanci, da barikanci, wannan ai shi ake cewa hisabi tun baka mutu ba, toh karku kuskura ku sawa yaranku suna munira, kuma inaso ku maidani abin kwatance ga yaranku da jikokai, ina cikin nadamar rayuwar danayi diga baya, Allah ka yafemin”.

A baya dai Muneerat ta kan Naɗi faifan Bidiyo da kalaman ɓatsa da sunan saida Maganin gyaran Maza ko na Mata, lamarin da yasanya jama’a ke ganin abinda take ya saɓa ma ƙa’ida harma akaita taƙaddama da ita, wani lokaci ma tace ta bar Musulinci kafin daga baya ta dawo.

Yanzu haka ta shiga kunci da tsananin rayuwa komai ya tsaya mata a cewar ta.

Wane fata zaku yi mata?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN