Labaran duniya

Ni Budurwa Ce Sabuwa Fil A Leda Dan Haka Duk Mai Son Aurena Yanzu A Shirye Na Ke, Cewar Wata Mata Bayan ta shafi Shekaru 70 batayi aure ba

Ni Budurwa Ce Sabuwa Fil A Leda Dan Haka Duk Mai Son Aurena Yanzu A Shirye Na Ke, Cewar Wata Mata Bayan ta shafi Shekaru 70 batayi aure ba

Daga Shuaibu Abdullahi, Dimokradiyya

Wata mata ƴar asalin Ƙasar Congo tace yanzu haka tana maraba da dukkan Namijin daya shirya Auren ta, matar wacce yanzu haka take cika shekaru 70 a duniya.

Matar mai suna Alphonsine Tawara, tace maza da dama sun nemi Auren ta lokacin tana da ƙuruciya, kuma tayi soyayyah mai tarin yawa sai dai a lokacin bata buƙatar aure.

Ta ɗauki hukuncin rashin yin Aure ne da wuri a kokarin ganin ta samarwa ƴan uwanta Karatu ingantacce.

Malamar makaranta ce ta kwashe shekaru mai tsawo tana karantarwa, bata da yaro ko guda amma dalubanta suna kwashe mata kewar rashin yaranta na jini.

Yanzu haka tana neman mijin Aure sai dai abun yana nema ya gagara, amma tana mai tabbatarwa da dukkan wanda zai Aure ta zai same ta sabuwa fil a leda kamar budurwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN