Labaran duniya

Ni Mutumin Kirki Ne, Kwata Kwata Sallah Ba Ta Wuce Ni A Kan Lokaci, Cewar Bello Turji

Ni Mutumin Kirki Ne, Kwata Kwata Sallah Ba Ta Wuce Ni A Kan Lokaci, Cewar Bello Turji

Ni Mutumin Kirki Ne, Sallah Ba Ta Wuce Ni A Kan Lokaci, Cewar Bello Turji

Daga Imam Indabawa Aliyu

Fitaccen ‘Danta’adda a Najeriya wanda ya yi kaurin suna wajen kashe mutane da garkuwa da su a dazukan da ke tsakanin jihar Zamafa da Sokoto wato Bello Turji ya bayyana cewa shi cikakken musulmi ne kuma sallah ba ta wuce shi a kan lokaci.

A yayin zantawarsa da kamfanin watsa labarai na Aminiya Bello Turji ya kalubalanci masu zargin sa da yi wa ‘yan mata fyade, zargin da ya ce sam babu gaskiya a cikinsa.

A cewarsa “Ka san akwai mutane da yawa, amma a ce ba mu bin addini, cikin ayar Alqur’ani akwai wata aya wacce ake cewa ”
إن الدين عند الله الإسلام”
Duk wani Malami a Najeriya da duniya ma ya san abin da wannan ayar ke nufi. A Izu na hamsin ne ma. Ka ga wanda bai bin addini ai bai kawo ta.

Sannan kuma ya yi maganar ba mu bin addini, addini ai ba nasa ba ne, na Allahn da ya halicce mu ne, ko mun yi bai ganewa. Sannan maganar da nake yanzu ai a masallaci ka iske ni kuma sallah na yi wa mahaliccina ba kaina na yi wa ba saboda ina gudun haduwata da shi. Bello Yabo karya yake da ya ce wai ya zauna da ni a Kurkuku. Karya yake idan ma Malami ne na gaske ko bai taba yi wa kowa karya ba, ni sai Allah ya isar min saboda ban taba zuwa Kurkuku ba.”

Ba wannan ne karon farko da Bello Tirji ke danganta kansa da addini ba. Ko a shekarar da ta gabata sai da Turji ya shirya kasaitaccen taron Mauludi wanda aka ce hatta mabiya Izala da ke kauyukan da suke karkashinsa suna biyan sa haraji sai da ya tilasta musu suka halarci taron Mauludin.

Ko a makon da ya wuce rahotanni sun ce Bello Turji ya fara kaddamar da hari kan ‘yan uwansa ‘yan bindiga bayan gwamnatin Zamfara ta yi masa afuwa, batun da gwamnatin ta Zamfara ta musanta shi cewa ba shi da makama ballantana tushe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN